Ba a Gama da Shari'ar Zabe Ba, Kotu Ta Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Kano 24 Kan Dalili 1 Tak

Ba a Gama da Shari'ar Zabe Ba, Kotu Ta Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Kano 24 Kan Dalili 1 Tak

  • Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan rusau, kotu ta yi hukunci kan wannan matsalar tare da rufe asusun gwamnatin jihar
  • Yayin hukuncin, Mai Shari'a, I. E Ekwo ya ba da umarnin rufe asusun bankunan gwamnatin jihar guda 24 da biliyan 30 na diyya
  • Wannan na zuwa ne bayan masu shaguna a Filin Idi da kuma kungiyar 'yan kasuwa ta shigar da kara kan zargin rashin bin ka'ida

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar kotun Tarayya ta umarci rufe asusun bankunan gwamnatin jihar Kano saboda rusau.

Kotun ta rufe akalla asusun gwamnatin jihar 24 da ke dauke da fiye da biliyan 30 saboda biyan diyyar wadanda aka yi wa rusau, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli, Hukumar NJC ta yi abu 1 don inganta bangaren shari'a

Kotu ta rufe asusun bankunan jihar Kano guda 24 kan rusau
Kotu ta sake yin hukunci kan rusau a jihar Kano. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke?

Mai Shari'a, I. E Ekwo ya ba da umarnin ne bayan shigar da kara da masu shaguna da 'yan kasuwa su ka yi kan rushe musu shaguna a watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu shigar da karar sun nuna rashin jin dadinsu da wannan lamari inda su ka ce ya sabawa doka kuma ba a bi ka'ida ba wurin rusau din.

Kotun ta rufe asusun bankunan har guda 24 wanda ya hada da na Babban Bankin Najeriya, CBN.

Daga bisani kotun ta dage ci gaba da sauraran shari'ar zuwa ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2024, cewar Daily Post.

Mene dalilin kai karar kotu?

Idan ba a manta ba tun bayan hawan Gwamna Abba Kabir ya fara aikin rusau wanda ya ke ganin an gina ba bisa ka'ida ba a jihar.

Kara karanta wannan

A wata daya: 'Yan sanda sun damke masu laifi 130 a Katsina, sun gurfanar da 61

Sai dai hakan ya bar baya da kura inda mutane da dama ke kalubalantar tsarin kan cewa rashin adalci ne da kuma durkusar da tattalin arzikin jihar.

Kungiyoyi da dama sun yi Allah wadai da wannan tsari na Abba Kabir inda su ka maka shi a kotu ganin yadda ya ke salwantar da dukiyar al'umma.

Abba Kabir ya kadu da rasuwar Asma'u Sani

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir ya nuna alhini kan rasuwar Asma'u Sani da ta sha fama da cutar daji.

Gwamnan a kwanakin baya ya yi alkawarin daukar nauyin jinyar yarinyar kafin rasuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel