Daga Karshe An bayyana Gaskiya Kan Sahihancin Zaman Gwamna Abba Kabir Yusuf Dan Jam'iyyar NNPP

Daga Karshe An bayyana Gaskiya Kan Sahihancin Zaman Gwamna Abba Kabir Yusuf Dan Jam'iyyar NNPP

  • Dokta Boniface Aniebonam ya fito ya yi magana kan sahihancin zaman Gwamna Abba Kabir Yusuf ɗan jam'iyyar NNPP
  • Boniface wanda shi ne ya kafa jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa gwamnan na Kano cikakken ɗan jam'iyyar ne
  • Ya yi nuni da cewa da ba cikakken ɗan jam'iyya ba ne da INEC ba ta bari ya shiga zaɓen gwamna ba na ranar 18, ga watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Boniface Aniebonam, wanda ya kafa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya roƙi dakarun da ke ciki da wajen jam’iyyar da su baiwa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano damar fuskantar mulki cikin kwanciyar hankali.

Aniebonam, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin amintattu na NNPP, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Legas, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

A Karshe, Jam'iyyar PDP ta fara ɗaukar matakan farfaɗowa daga bugun da ta sha a zaben 2023

Boniface ya ce Abba Kabir cikakken dan NNPP ne
Dokta Boniface ya ce Gwamna Abba cikakken dan NNPP ne Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kalaman nasa na zuwa ne biyo bayan cece-kucen da aka samu kan hukuncin da kotu ta yanke na korar Gwamna Abba da zamansa ɗan jam’iyyar NNPP a zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Boniface ya tabbatar da zaman Gwamna Abba ɗan NNPP

Aniebonam, a martanin nasa na baya-bayan nan, ya ce:

“Ina kuma sake bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, cikakken ɗan jam’iyyar NNPP ne."
"Idan da ba ɗan jam'iyya ba ne, da NNPP ba za ta gabatar da shi ga ƴan asalin Kano ta hanyar INEC domin zaɓen gwamna a 2023 ba."
"Idan da shi ba mamba ba ne kuma jam’iyyar NNPP ta gabatar da shi domin gudanar da zaɓe, ina tsammanin da INEC ba za ta bari ya shiga zaɓen ba."

Kara karanta wannan

Kano: Wasu shugabannin NNPP sun juya wa Gwamna Abba baya, sun amince da hukuncin kotu

"Kuma ina sake nanata wa, jam’iyyar siyasa ce kawai ke tantance zama ɗan jam'iyya, ba INEC ko wani daban ba."

Da yake kira da a samar da zaman lafiya da adalci a Kano, wanda ya kafa NNPP ya bayyana fatan cewa kotun koli za ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Lauyoyi Sun Gano Matsala a Hukuncin Tsige Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu lauyoyi daga jihohi 19 na Arewacin Nakeriya sun soki hukuncin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.

Lauyoyin a ƙarƙashin ƙungiyar lauyoyin Arewa sun bayyana kuskuren da aka samu a sakin layi biyar na cikin kwafin takardun hukuncin a matsayin wanda ba a yafe wa kuma ya jefa ɓangaren shari'a cikin kokwanto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng