Rikicin Kano: DSS Za Su Binciki Rabiu Musa Kwankwaso? Bayanai Sun Fito

Rikicin Kano: DSS Za Su Binciki Rabiu Musa Kwankwaso? Bayanai Sun Fito

  • Ƙungiyar yaƙi da ta'addanci ta NCAT ta jawo hankalin hukumar DSS kan halin ɗar-ɗar da ake ciki a Kano
  • Ƙungiyar ta buƙaci hukumar DSS da ta gayyaci Kwankwaso domin ya amsa tambayoyi kan zanga-zangar da ake yi a Kano
  • Ƙungiyar ta yi nuni da cewa gaggatar Ƙwankwaso ya zama dole saboda ƴan Kwankwansiyya na ƙoƙarin tada tarzoma kan tsige Gwamna Abba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata ƙungiyar yaƙi da ta’addanci da ke aiki a ƙarƙashin ƙungiyar National Coalition Against Terrorism (NCAT) ta buƙaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta gaggauta gayyatar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ƙungiyar ta buƙaci DSS ta gayyaci Kwankwaso ne domin amsa tambayoyi dangane da zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan, da cin zarafin ƴan ƙasa da kuma kai hare-hare kan ɓangaren shari'a.

Kara karanta wannan

MURIC ta yi Allah wadai da kisan masu maulidi a Kaduna, ta fadi bukatunta

An bukaci DSS sun binciki Kwankwaso
An yi kira ga DSS su binciki Kwankwaso kan zanga-zanga a Kano Hoto: DSS/Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

Meyasa ƙungiyar ke son a gayyaci Kwankwaso?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta bayyana fargabar cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, ƙungiyar Kwankwaso da aka fi sani da Kwankwasiyya za ta iya tayar da tarzoma a ƙasar nan biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na tsige Gwamna Abba Yusuf.

A yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Disamba, Terrence Kuanum, kodinetan ƙungiyar na ƙasa, ya kuma ƙara da cewa, Kwankwasiyya na shirin kai hare-hare tare da cin mutuncin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, don haifar da tarzoma a Kano da Abuja.

Kuanum ya bayyana cewa tun kafin hukuncin kotun zaɓe da ya tsige Gwamna Abba, ɓangaren shari'a musamman alƙalai suka ria fuskantar barazana daga wajen ƴan Kwankwasiyya.

NCAT ta yi magana kan zanga-zanga a Kano

Ƙungiyar ta bayyana cewa tuni aka fara haka ta hanyar yin zanga-zangar da wasu son tada ƙayar baya suke yi domin nuna adawa da hukuncin kotu na tsige Gwamna Abba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar Labour Party ta caccaki Peter Obi, bayanai sun fito

Ƙungiyar ta ce:

"Ba tare da wata shakka ba, muna kira ga shugaban DSS da ya gaggauta gayyatar Rabi’u Musa Kwankwaso domin yi masa tambayoyi kafin ƴan Kwankwasiyya su ƙona ƙasar nan."
"A matsayinsa na tsohon Gwamna, tsohon ministan tsaro da kuma Sanata, yana iya haifar da tashin hankali kuma ya jajirce akan yin hakan."
"Muna kuma ba da shawarar a kama tare da yi wa waɗannan masu son tayar da hankalin da tuni Mista Kwankwasiyya ya haɗa baki da su domin jagorantar tashe tashen hankula a Abuja, Mista Ladipo Johnson, Ladipo Olayoku, Alhaji Abba Kawu, Prince Nwaeze Onu, Tunde Oke, Badmus Kilamuwaye, Olufemi Oguntoyinbo da sauransu."

An Bayyana Sahihancin Zaman Gwamna Abba Ɗan NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wanda ya kafa jam'iyyar NNPP, Dokta Boniface Aniebonam ya yi magana kan taƙaddamar zaman Gwamna Abba ɗan jam'iyyar NNPP.

Boniface ya yi nuni da cewa gwamnan cikakken ɗan jam'iyyar NNPP ne wanda hakan ya sanya har ya yi takarar gwamnan Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel