Kano: Yarinyar da Abba Kabir Ya Dauki Nauyin Jinyarta Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Bayanai Sun Fito

Kano: Yarinyar da Abba Kabir Ya Dauki Nauyin Jinyarta Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake shirye-shiryen fitar da Asma'u Sani kasar waje don yi mata aiki, Allah ya karbi rayuwarfa a yau
  • Marigayiyar, Asma'u ta sha fama da jinyar cutar daji wanda hakan ya jawo hankalin mutane ciki har da Gwamna Abba Kabir
  • Yayin wata ziyara da gwamnan ya kai asibitin da ta ke, ya ba da gudummawar naira miliyan 1.5 don kulawa da lafiyarta

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Asma'u Sani, yarinya 'yar shekaru takawa da Abba Kabir ya dauki nauyin jinyarta ta rasu.

Marigayiyar ta sha fama da cutar daji wanda ya dauki hankalin gwamnan tare da daukar nauyin jinyarta.

Abba Kabir ya kadu da samun labarin mutuwar Asma'u Sani
Abba Kabir ya tura sakon jaje ga iyayen Asma'u Sani. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Yaushe Asma'u Sani ta rasu?

Asma'u ta rasu ne a babban asibitin Dala inda a nan ta ke jinya kafin kokarin fita da ita waje, cewar TVC News.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Gombe rasuwa da yammacin yau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir ya ba da gudummawar naira miliyan 1.5 bayan ya kawo ziyara asibitin don duba yarinyar.

Gwamna ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba ta gudunmawa har zuwa lokacin da za ta samu lafiya da sauran bukatunta.

Hadimar Gwamna Abba Kabir a bangaren jin kai, Fauziyya D. Sulaiman ita ta bayyana haka a shafin Facebook a yau Laraba 6 ga watan Disamba.

Wane martani Abba Kabir ya yi kan rasuwar Asma'u Sani?

Wannan na zuwa ne yayin da aka kammala shirye-shiryen fitar da ita kasar Indiya don yi mata aiki.

Yayin da ya ke martani, Gwamna Abba Kabir ya ce ya kadu da samun labarin mutuwar Asma'u Sani da safiyar yau.

Gwamna ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Laraba 6 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya kirkiri asibitin tafi da gidanka don amfanin Kanawa, ya tura sakon gargadi

Ya yi addu'ar ubangiji ya mata rahama kuma ya bai wa iyayenta da su hakurin jure wannan rashi.

Abba Kabir ya dauki nauyin jinyar Asma'u Sani

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya kai ziyara asibitin Dala inda ya ci karo da wata yarinya mai suna Asma'u Sani.

Gwamnan ya ba ta gudummawar naira miliyan 1.5 don yi mata aiki yayin da ta ke fama da cutar daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel