Kano: Lauyoyin Jihohi 19 Sun Kara Gano Wata Matsala a Hukuncin Tsige Abba, Sun Bayyana Mafita

Kano: Lauyoyin Jihohi 19 Sun Kara Gano Wata Matsala a Hukuncin Tsige Abba, Sun Bayyana Mafita

  • Kungiyar matasan lauyoyin jihohin arewa 19 sun caccaki hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnan Kano
  • Mai magana da yawun ƙungiyar, Yusuf Ibrahim, ya bayyana cewa hukuncin ya nuna rashin adalci ƙarara
  • Kungiyar ta kuma roki a sake komawa kan tebur a gyara kundin dokokin zaben da ake amfani da su a yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Ƙungiyar matasan lauyoyin arewa ta soki hukuncin kotun ɗaukaka kara wanda ya tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Lauyoyin, waɗanda suka fito daga jihohin arewa 19, sun caccaki hukuncin wanda ya bayyana Nasiru Gawuna a matsayin zababben gwamnan Kano, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wakilan Gwamnatin Kaduna sun dira garin da sojoji Suka kashe bayin Allah a taron Maulidi

Mai magana da yawun matasan lauyoyin arewa, Yusuf Ibrahim.
Kano: Kungiyar Lauyoyi Ta Soki Hukuncin Tsige Abba Kabir Yusuf Hoto: channelstv
Asali: UGC

Sun kuma bayyana kuskuren da aka samu a sakin layi biyar na cikin kwafin takardun hukuncin a matsayin wanda ba a yafe wa kuma ya jefa ɓangaren shari'a cikin kokwanto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun ƙungiyar matasan lauyoyin arewa, Yusuf Ibrahim, ne ya faɗi haka yayin da yake jawabi ga manema labarai ranar Lahadi a Kaduna.

Ya ce hukuncin da aka yanke a zaben gwamnan Kano, ya nuna rashin adalci karara, kuma mafi mahimmanci, zambar siyasa da canza zaɓin da mutanen Kano suka yi.

A rahoton Leadership, Ibrahim ya ce:

"Maganar gaskiya, a yanzu ba ka da tabbacin hukuncin da kotu za ta yanke a kasar nan, ko da kuwa kai masanin shari’a ne, duk iliminka a fannin.”

Bisa haka ƙungiyar, wadda ta kunshi lauyoyi masu zaman kansu, ta sadaukar da kanta kyauta domin taimakawa Gwamna Abba wajen kwato haƙƙinsa a kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya ƙara samun gagarumin goyon baya da ka iya sa ya lallasa Abba a Kotun Koli

Ta kuma jaddada kwarin guiwar cewa kotun Allah ya isa zata yi adaci, ta tabbatar da Abba Gida-Gida a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen Kano a watan Maris.

Menene mafita kan faruwar irin haka?

Da yake nasa jawabin kan kes din gwamnan Kano, wani mamban ƙungiyar, Usman Ashafa, ya bukaci a sake komawa a gyara kundin dokokin zaɓe.

Ya roƙi cewa daga cikin gyaran da za a yi wa dokar zaɓe, ya kamata a haramta wa kotu tsoma baki a al'amuran da suka shafi gabanin zaɓe idan har an bayyana wanda ya samu nasara.

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Mutane 7 a Manyan Muƙamai

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabuwar shugabar hukumar shige da fice da mataimaka shida.

A wata sanarwa ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023, naɗin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262