Kano: Wasu Shugabannin NNPP Sun Juyawa Gwamna Abba Baya, Sun Amince da Hukuncin Kotu

Kano: Wasu Shugabannin NNPP Sun Juyawa Gwamna Abba Baya, Sun Amince da Hukuncin Kotu

  • Shugabannin NNPP karkashin jagorancin Major Agbo sun juyawa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya a shari'ar zaben Kano
  • Da yake hira da ƴan jarida a Abuja, shugaban NNPP na ƙasa ya bayyana inda aka samu matsala har kotu ta ce Abba ba ɗan jam'iyya bane
  • Ya kuma yi tir a tashin-tashinar da ta biyo baya a birnin Kano da sunan zanga-zanga, yana mai cewa jam'iyyar tana goyon bayan tsarin shari'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wasu shugabannin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) sun juyawa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya, sun goyi bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

A cewar jam'iyyar, Abba Gida-Gida bai zama cikakken mamban NNPP ba a lokacin da aka yi zaɓe kamar yadda kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana sahihancin zaman Gwamna Abba Kabir Yusuf dan jam'iyyar NNPP

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.
Kano: NNPP Ta Goyi Bayan Kotun Daukaka Kara, Ta Ce Abba da Dan Jam'iyya Bane Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Tsagin NNPP wanda Major Agbor ke jagoranta ne ya yi wannan ikirarin a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da ƴan jarida, Dakta Agbor ya bayyana damuwarsa kan karuwar tashin-tashina a jihar Kano bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Ya koka kan yadda rashin zaman lafiya ke ƙaruwa a Kano kama daga zanga-zanga, tunzura jama'a, munanan kalamai da toshe hanyoyi suka kai wani mataki mai ban tsoro.

Ya ce jam’iyyar NNPP tana matukar goyon bayan doka da kuma shari'a, tare da nuna rashin amincewa da duk wani hari da sukar da wasu ke yi wa tsarin shari’a.

"Muna Allah wadai da barazanar da wasu korarrun mambobi suka yi wanda ya tilastawa alkalan kotun zabe barin Kano," in ji shi.

Abba ya saɓa wa kundin tsarin mulkin NNPP

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya ƙara samun gagarumin goyon baya da ka iya sa ya lallasa Abba a Kotun Koli

Agbor ya yi nuni da cewa hukuncin kotuna biyu cewa Gwamna Abba Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne ya samo asali ne daga rashin bin ƙa'idar kundin tsarin mulkin jam’iyya.

A halin yanzu, Gwamnan Kano ya ɗaukaka kara zuwa kotun koli bayan rashin nasara a kotun ɗaukaka ƙara.

Lauyoyin Jihohi 19 Sun Kara Gano Wata Matsala a Hukuncin Tsige Abba

A wani rahoton kuma Kungiyar matasan lauyoyin jihohin arewa 19 sun caccaki hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnan Kano.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Yusuf Ibrahim, ya bayyana cewa hukuncin ya nuna rashin adalci ƙarara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262