Korar Kwankwaso: Shugaban NNPP Ya Fadi Dalilin Korar, Ya Bayyana Irin Yarjejeniyar da Su Ka Kwance

Korar Kwankwaso: Shugaban NNPP Ya Fadi Dalilin Korar, Ya Bayyana Irin Yarjejeniyar da Su Ka Kwance

  • Shugaban jam'iyyar NNPP ya bayyana dalilin korar dan takarar jam'iyyar a zaben shugaban kasa, Rabi'u Kwankwaso
  • Agbo Major ya ce sun fuskanci Kwankwaso da mukarrabansa na son kwace jami'yyar daga wadanda su ka kirkire ta
  • Major ya ce yarjejeniya su ka yi don kawai su tsaya zabe a 2023 da sharadin za su iya dawo wa bayan zabe ko su wuce gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar NNPP, Agbo Major ya bayyana dalilin da ya sa su ka kori Rabi'u Kwankwaso a jam'iyyar.

Major wanda ya ce a yanzu shi ne shugaban jam'iyyar ta NNPP ya ce Kwankwaso na son kwace akalar jami'yyar ce daga hannunsu.

Kara karanta wannan

Manyan Arewa: Take-taken Tinubu sun nuna bai damu da gyara tsaron Arewa ba

NNPP ta fadi dalilin korar Rabiu Kwankwaso daga jami'yyar
An bayyana babban dalilin korar Rabiu Kwankwaso daga NNPP. Hoto: Rabi'u Kwankwaso.
Asali: Facebook

Wane dalili ne ya sa aka kori Kwankwaso a NNPP?

Agbo ya ce wannan dalili ya sa su ka kori Kwankwaso daga jam'iyyar ganin yadda ya dauko na hannun damansa su na son yin karfa-karfa a jami'yyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne yayin da gidan talabijin na Channels inda ya ce sun kirkiri jami'yyar amma wani na son kwace ta a hannunsu.

Ya ce:

"Cewa su ke wannan wanda ya kirkiri jami'yyar ba shi da matsala mu kwace ragamar jami'yyar kawai.
"Wannan shi ne abin da su ke fada inda su ke cewa shi mai jami'yyar ya na da fahimta, mu kuma mu ka ki amincewa da haka saboda kishin jami'yya."

Wace yarjejeniya NNPP ta kulla da Kwankwaso?

Agbo ya ce Kwankwaso da mukarrabansa sun shiga jam'iyyar ce a bara bayan an yi yarjejeniyar ba su damar tsayawa takara.

Kara karanta wannan

NDLEA ta gano katafaren gonar da ake noman wiwi a Sokoto, ta cafke mutum daya

Ya kara da cewa:

"Sun shiga jam'iyyar ce kawai saboda dalilin zabe bayan mun yi yarjejeniyar ba su damar tsayawa takara a 2023."

Major ya ce sun yi yarjejeniyar da cewa bayan zabe za su iya tafiya inda su ke so ko su dawo a ci gaba da tafiya tare, cewar Daily Post.

Ya ce amma bayan gama zabe sai su ka fuskanci dabi'unsu inda su ka gane tafiyar ba za ta yi daya ba.

NNPP ta amsa gayyatar Atiku na hadaka

A wani labarin, Jami'yyar NNPP a Najeriya ta amince da tayin dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar kan hadaka.

Atiku a kwanakin baya ya yi kira ga jam'iyyun adawa don su yi hadaka kan kwace mulki a hannun jami'yyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel