"Muna Fatan Nasara": Hadimin Abba Ya Magantu Yayin Da Kotun Koli Ke Shirin Zama Kan Shari'ar Kano

"Muna Fatan Nasara": Hadimin Abba Ya Magantu Yayin Da Kotun Koli Ke Shirin Zama Kan Shari'ar Kano

  • Kotun koli za ta soma yin zama domin warware gardamar da ake yi a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano
  • Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara da kotu ta tsige shi daga kujerar gwamnan Kano a cikin watan Nuwamba
  • Alkalai sun ce ‘dan takaran APC watau Nasiru Yusuf Gawuna ne wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kotun koli za ta fara yin zama domin sauraron shari’ar zaben gwamnan Kano da aka yi a 2023 wanda ya ja hankali.

Jita-jita daga Aminiya ya tabbatar da kotun koli za ta fara sauraron karar da Abba Kabir Yusuf ya daukaka na shari’ar zabe.

Bayanai sun nuna ba a tsaida lokacin da za a fara sauraron shari'ar a babban kotun kasar ba, daga nan a shirya yin hukunci.

Kara karanta wannan

Kwanaki 5 da hukuncin Kotun Koli, Sarakuna 4 sun ki taya Abba murnar galaba kan APC

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya je kotun koli Hoto: @SanusiBature
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Gida Gida v Nasiru Gawuna a kotun koli

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun korafin zabe, inda Alkalai uku su ka tsige Abba Kabir Yusuf daga mulki.

Mai girma Abba Kabir Yusuf bai yarda da hukuncin da aka yi ba, ya roki kotun koli ta tabbatar da zaben da hukumar INEC ta yi.

Daily Nigerian ta ce Mai shari’a Moore Aseimo A. Adumein da ya jawo rudanin CTC ya na kan hanyar zama Alkalin kotun koli.

'NNPP za tayi nasara' – Hadimin Abba

Hassan Sani Tukur shi ne mai taimakawa Abba Kabir Yusuf a kafofin sadarwa na zamani, ya shaidawa Legit cewa yana fatan nasarar mai gidansa.

Da mu ka zanta da shi, hadimin gwamnan ya ce NNPP ta doke APC war-was a Kano a zaben bana, amma sai aka buge da wasu hujjoji a kotun zabe.

Kara karanta wannan

Bayan ya koma Kano, Gwamna Abba ya faɗi mutum 1 da ya cancanci yabo kan hukuncin kotun ƙoli

Mukarrabin gwamnan ya ce tun farko ya kamata kotun korafin zabe ta yi watsi da karar ganin irin hujjojin da jam’iyyar APC ta kafa hujja da su a kotu.

A cewar Hassan Tukur, ba ayi adalci wajen zaftarewa NNPP kuri’u 165,616 da INEC ta kirga ba.

Mai bada shawarar ya nuna mamakinsa ga yadda kotun daukaka kara ta dawo da batun zama ’dan NNPP, yana mai sa ran kotun koli ta yi watsi da shi.

Layan NNPP ya daukaka kara a kotun koli

Lauyan da yake kare Gwamnan, Wola Olanipekun ya kalubalanci yadda kotu ta zaftare kuri’u 165, 000 da NNPP ta samu.

Wola Olanipekun SAN ya kuma ce kotun daukaka kara ba ta da hurumin shiga maganar zaman Abba ‘dan jam’iyyar NNPP.

Abba ya yi nadin mukamai a Kano

Ana haka aka ji Abba Kabir Yusuf ya sanar da nadin karin hadimai 13 a gwamnati, Salisu Hotoro ya fitar da labarin a shafinsa.

Kara karanta wannan

Abba ya nunawa duniya masoyansa a Kano da ya dawo bayan hukuncin Kotun Koli

Darekta Janar na yada labarai da hulda da jama’a, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da jawabi na musamman a safiyar Alhamis.

Wadanda aka nada sun hada da masu bada shawara a kan harkokin Yarbawa, Ibo da sauran mutanen Arewa da ke zama a Kano.

  1. Dr. Ibrahim Garba Muhammad
  2. Hon. Dankaka Hussain Bebeji
  3. Cif Chukwuma Innocent Ogbu
  4. Abdussalam Abdullateef
  5. Mr. Andrew Ma'aji
  6. Alh. Usman Bala
  7. Hajiya A'in Jafaru Fagge
  8. Hon. Isah Musa Kumurya
  9. Dr. Naziru Halliru
  10. Barr. Maimuna Umar Sharifai
  11. Hon. Danladi Karfi
  12. Gwani Muhammad Auwal Mukhtar
  13. Alhaji Ada'u Lawan

Abba ya nada SSG na rikon kwarya

Ana da labari cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci Abdullahi Musa ya lura da ofishin Sakataren gwamnatin Kano na ‘yan makonni.

Musa zai cike gurbin Dr. Abdullahi Baffa Bichi wanda ya tafi asibiti a Saudi Arabiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng