“Ina Bakin Ciki Matuka”: Gwamnan Kano Ya Yi Alhinin Mutuwar Asma'u Sani Da Kansa Ta Kashe

“Ina Bakin Ciki Matuka”: Gwamnan Kano Ya Yi Alhinin Mutuwar Asma'u Sani Da Kansa Ta Kashe

  • Asma'u Sani, yarinya yar shekaru 8 da ta ja hankalin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a soshiyal midiya bayan an nemi taimakon naira miliyan 1.5 na yi mata aiki ta rasu
  • Legit Hausa ta tattaro cewa Asma'u ta rasu ne a ranar Larabam 6 ga watan Disamba, a asibitin kashi na kasa, Dala, inda take jinya
  • Yarinyar dai na dauke da cutar kansa wacce ta kama kafarta ta dama kuma ana yi mata magani a asibitin kashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Kano, ya nuna bakin ciki matuka kan mutuwar Asma'u Sani, yarinyar da ke fama da cutar kansa a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Kano: Yarinyar da Abba Kabir ya dauki nauyin jinyarta ta riga mu gidan gaskiya, bayanai sun fito

Legit Hausa ta samu labarin cewa Asma'u ta rasu ne a safiyar ranar Larba, 6 ga watan Disamba.

Gwamnan Kano ya yi alhinin mutuwar Asma'u
“Ina Bakin Ciki Matuka”: Gwamnan Kano Ya Yi Alhinin Mutuwar Karamar Kawarsa Da Kansa Ya Kashe Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnan Kano ya yi alhinin mutuwar yar shekaru 8

Kamar yadda TVC ta rahoto, yarinyar ta rasu ne a asibitin kashi na kasa da ke Dala a Kano inda take jinya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Nuwamba ne gwamnan Kano ya ziyarci Asma'u, wacce ya kira da "karamar kawata", yayin da take ci gaba da farfadowa kafin tafiyarta kasar Indiya don ci gaba da jinya.

Yarinyar mai shekaru takwas ta ja hankalin Gwamna Yusuf a dandalin soshiyal midiya bayan an nema mata taimakon naira miliyan 1.5.

Gwamnan ya rubuta a dandalinsa na Twitter

"Ina cike da bakin cikin jin labarin mutuwar Asma'u, a safiyar nan.
"Allah madaukakin sarki ya saka mata da Jannatul Firdaus. Kuma Allah ya ba danginta da mu duka karfin jure rashinta."

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi ganawar sirri da Wike kan zaben 2027, rahoto

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

A wani labarin, mun ji cewa mai girma Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa Sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya tafi asibiti a ketare.

A wani jawabi da ya fito daga ofishin Sanusi Bature Dawakin Tofa, an fahimci Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya je ganin likita a Saudi Arabiya.

Kamar yadda Sakataren yada labaran gwamnan Jihar Kano ya bayyana, Abdullahi Musa zai kula da ofishin Sakataren gwamnatin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel