Yan bindiga
Rundunar tsaron Najeriya ta cigaba da da hada kai da sojojin Najar wajen yaki da 'yan ta'adda duk da sabanin siyasa da aka samu tsakanin Tchiani da Tinubu.
Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sen. Lawal Adamu Usman ya sha da kyar bayan wasu miyagu sun kai masa hari a daren jiya Laraba 1 ga watan Janairun 2024.
Sojojin Najeriya sun yi kofar rago ga Bello Turji yayin da suka kashe manyan na hannun damansa suka kama masu taimaka masa a Sokoto, Zamfara da Kebbi.
Wasu tsagerun ƴan bindiga sun shiga kauyen Kuki da tsakar rana ido na ganin ido, ana zargin sun halaka wata ƙaramar yarinya yar kimanin shekara 7 a Kaduna.
Mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya fadi matakan da ya kamata a dauka kan rashin da tsaro inda ya ce dole a nemi taimakon al'umma.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fitar da rahoto kan nasarorin da ta samu a 2024, ta kama 'yan daba, 'yan fashi da masu garkuwa da mutane da karin mutane 2,425
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi wa motar fasinjoji kwanton bauna a jihar Zamfara. 'Yan bindiga sun ta sa keyar dukkanin fasinjojin zuwa cikin daji.
Sojojin Najeriya sun kashe wasu manya manyan shugabannin ‘yan bindiga da suka hada da Halilu Sububu a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2024.
Shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, ya yi kunnen uwar shegu da rokon da wasu shugabannin Fulani suka yi masa. Ya ci gaba da kai hare-hare a Zamfara.
Yan bindiga
Samu kari