Yan bindiga
Yayin da rashin tsaro ke sake taɓarɓarewa a Zamfara, Kungiyar NDYC ta bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta baci a jihar saboda yawaitar kashe-kashe.
Wasu da ba a san su waye ba sun yi harbe harbe wajen taron nuna goyon baya ga ministan Abuja, Nyesom Wike. Tun farko dama gwamnati ta hana taron.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a juhar Zamfara. Miyagun wadanda suka kai hare-haren a wasu kauyuka uku, sun hallaka mutane 28.
Rundunar sojin Najeriya ta kama wani dan bindiga da aka dade ana nema ido rufe mai suna Dogo a jihar Taraba. An kama wani mutum mai karya soja a Taraba.
‘Yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe sabon ango a Nasarawa, tare da sace amaryarsa. A Edo kuma, 'sun kashe magidanci tare da sace matarsa da ‘yar uwarta.
Wasu 'yan bindiga da ba san ko wanene ba, sun yi awon gaba da wani limamin cocin Katolika a jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun kutsa har gida sannan suka sace shi.
Rundunar 'yan sandan jihar Filato ta bayyana sunayen mutane uku da aka kama dauke da bindiga. An kama mutanen ne bayan an sha fama da hare haren 'yan bindiga jihar.
An samu sauki bayan fitaccen jagoran 'yan bindiga, Harisu Babba Yauni, ya mutu tare da wasu daga cikin yaransa guda 10 a rikicin cikin gida da ya auku a Katsina.
Rahotanni sun tabbatar cewa yan bindiga sun kai hari a lokacin sallar Isha a Tudun Malamai da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.
Yan bindiga
Samu kari