Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Kai Hari a Jihar Nasarawa, Sun Sace Daliban Firamaren Gwamnati

Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Kai Hari a Jihar Nasarawa, Sun Sace Daliban Firamaren Gwamnati

  • Rahoton da muke samu daga jihar Nasarawa ya bayyana cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai
  • An ce sun sace yaran ne da sanyin safiyar ranar Juma'a 20 ga watan Janairun 2023 da muke ciki
  • Ya zuwa yanzu dai ba a san adadin daliban da aka sace ba, amma rundunar 'yan sanda ta tababatar da faruwar lamarin

Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun sanyin safiyar ranar Juma’a sun kai mummunan hari makarantar Firamaren Gwamnati da ke Alwaza a karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa.

Ana zargin ‘yan bindigan sun yi awon gaba da wani adadi na dalibai na makarantar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

An ce ‘yan bindigan sun saraf sun sace daliban ne da safe a daidai lokacin da suke zuwa makarantar da safe.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tagwayen Abubuwa Masu Fashewa Sun Tashi a Wurin Kamfen din APC a Fatakwal, 3 Sun Jigata

Yadda 'yan bindiga suka sace dalibai a Nasarawa
Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Kai Hari a Jihar Nasarawa, Sun Sace Daliban Firamaren Gwamnati | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu dai ba a san inda ‘yan bindigan suka yi da daliban ba, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya bayyana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Rahman Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar rundunar ‘yan sanda, gamayyar rundunar tsaro ta ‘yan sanda, sojoji da ‘yan banga na ci gaba da sintiri don gano inda ‘yan bindigan suka shiga.

Ba wannan ne karon farko da ake sace dalibai ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa a yankuna daban-daban na Arewacin kasar.

'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe

A wani labarin na daban, kunji yadda 'yan bindiga suka sace wasu dalibai biyar biyar a garin Tsafe a wata kwalejin kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Katsina: An Yi Nasarar Kubutar da Daya Daga Cikin Mutanen da Yan Bindiga Suka Sace a Wajen Bauta

Wannan lamari dai ya faur ne a jihar Zamfara, inda 'yan bindiga ke yawan kai hare-hare a 'yan shekarun nan, kamar yadda jarida Channels Tv ta ruwaito.

Majiya ta bayyana cewa, 'yan bindigan sun dura dakin gwanan daliban ne da ke wajen makarantar tare da yin awon gaba dasu zuwa wani wurin da ba a sani ba.

A cewar majiyar, babu ta inda 'yan bindigan za su iya kutsawa don shiga makarantar saboda tarin jami'an tsaro da ke jibge a haraba da bakin kwalejin kiwon lafiyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel