'Yan Bindiga Sun ki Karbar N5.3m na Tsofaffin Kudi, Sun ce Sun Dab da Lalacewa

'Yan Bindiga Sun ki Karbar N5.3m na Tsofaffin Kudi, Sun ce Sun Dab da Lalacewa

  • 'Yan bindigan da suka sace jama'a a jihar Kaduna sun ki karbar tsofaffin takardun N5.3 miliyan da aka kai musu na fansa a makon da ya gabata
  • Shugaban 'yan bindigan yace kudin suna dab da zama takardun banza, don haka a siyo musu kayan abinci, kwayoyi da giya da su
  • Ya saki wasu mutum 5 inda ya rike sauran yace sai an tattaro musu sabbin takardun kudin da aka canza sannan zai karba kudin fansarsu

Kaduna - Wasu 'yan bindiga sun ki karbar N5.3 miliyan na kudin fansa da aka biya su da tsofaffin kudi inda suka ce lokacin da za a daina karbarsu na karatowa.

Kaduna bandits
'Yan Bindiga Sun ki Karbar N5.3m na Tsofaffin Kudi, Sun ce Sun Dab da Lalacewa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta gani cewa, shugaban 'yan bindigan da ya kai farmaki yankunan Azara, Jangala da Kadara a jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Disamban 2022, ya sace mutum 37, ya bukaci 'yan uwan wadanda ya sace da su koma da tsofaffin kudin da suka kai masa na fansa.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mabarata Sun Dire Gefe, Sun Daina Karbar Tsofaffin Takardun Naira

A maimakon hakan, ya bukaci kayan abinci, magunguna da giya domin ya saki masu jego biyu da wasu maza uku daga cikin mutum 11 da yayi garkuwa da su a yankin Azara da ke karamar hukumar Kachia.

Wani 'dan uwan daya daga cikin wadanda aka sacen mai suna Haruna Shuaibu, ya tabbatar da sakin matan biyu da mazan uku a wayar salula da suka yi da Daily Trust a ranar Laraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi bayanin cewa, 'yan uwan wadanda aka sace sun hada N5.3 miliyan na kudin fansa amma shugaban 'yan bindigan ya ki karba yayin da ya gane cewa tsofaffin kudi ne.

Yace:

"A makon da ya gabata, iyalai da 'yan uwan wadanda aka sace sun hada kudin fansa. Kuma bayan an kai musu, shugabansu ya ki karba inda yace tsofaffin kudi ne wadanda nan babu dadewa za su daina aiki.

Kara karanta wannan

Cikin sauki: Yadda za ku yi ku rabu da tsoffin Naira, ku sami sabbi a kusa daku

"Ya umarci iyalan da su yi amfani da kudaden wurin siya masa kayan abinci da kwayoyi."

Ya kara da cewa, 'yan uwan sun dawo da kudin sun siya kayan abinci, miyagun kwayoyi da katan-katan din giya kafin a saki wasu daga cikinsu a ranar Asabar.

Shuaibu ya kara da cewa, sauran wadanda aka sacen har yanzu suna hannun 'yan bindigan yayin da suka jaddada cewa sai sabbin kudi za su karba na fansa.

Babu martani daga kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna kan wannan lamarin.

Soji sun yi wa mayakan ISWAP luguden wuta a Borno

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya na sama da na kasa a jihar Borno sun yi wa 'yan ta'addan ISWAP luguden wuta inda suka halaka da dama a ciki.

An tattaro yadda mayakan ta'addanci suka kai wa dakarun farmakin kwantan bauna a Damboa amma sojin suka dakile.

Asali: Legit.ng

Online view pixel