Tashin Hankali Yayin da Aka Sheke Mambobin APC 2 Suna Tsaka da Taro a Jihar Ebonyi

Tashin Hankali Yayin da Aka Sheke Mambobin APC 2 Suna Tsaka da Taro a Jihar Ebonyi

  • An samu wani tashin hankali yayin da wasu 'yan bindiga suka kai farmaki kan wasu mambobin jam'iyyar APC
  • An hallaka mutum biyu nan take, wasu biyu kuma sun samu raunuka munanan bayan faruwar lamarin
  • Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana sunayen wadanda lamarin ya rutsa dasu ba, amma an ce 'yan APC ne

Jihar Ebonyi - Rahoton da jaridar Vanguard tace ta samo ya bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun farmaki al’ummar karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi, inda suka kashe mutum biyu da ake kyautata zaton mambobin APC ne.

An tattaro cewa, lamarin ya faru ne a yayin da mambobin APC a yankin ke zaman tattaunawa a jiya Juma’a 20 ga watan Janairun 2023.

A cewar rahoton, ‘yan bindigan sun bude wuta ne kan mambobin na APC da ke gudanar zaman tattaunawa a garin.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta Sanar da Sabon Farashin Litar Fetur, An Amince da Karin 8.8% a Najeriya

An kashe 'yan APC a Ebonyi
Tashin Hankali Yayin da Aka Sheke Mambobin APC 2 Suna Tsaka da Taro a Jihar Ebonyi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

‘Yan bindigan, wadanda aka ce sun zo ne su biyu a kan babur sun aikata barnar tare da tserewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda lamarin ya faru

Wata majiya da jaridar ta bayyana ta ce, lamarin ya faru ne a kauyen Mkpuma Akpatakpa da ke karamar hukumar ta Izzi.

An tabbatar da mutuwar mutanen biyu, yayin da wasu biyu ma suka samu raunuka ana kula dasu a asibitin koyarwa na Alex Ekwuenme a birnin Abakaliki.

Da yawa suna cike da mamakin ko watakila harin na da alaka da abin da ka iya biyo ba baya a zaben 2023 mai zuwa.

Ya zuwa yanzi dai ana ci gaba da bincike don gano musabbabin harin da kuma gano wadanda aka kashe, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Kai Hari a Jihar Nasarawa, Sun Sace Daliban Firamaren Gwamnati

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

A wani labarin kuma, kunji yadda wasu tsagerun 'yan bindiga suka yi awon gaba da wani adadi na daliban firamare a jihar Nasarawa.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an sace yaran ne da sanyin safiyar jiya Juma'a lokacin da suke zuwa makaranta a makarantar da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da adadin daliban ba, amma hukumar 'yan tsanda ta tabbatar da faruwar mummunan lamarin da aka saba yi a Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel