Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Bindige Kansila Har Lahira A Jihar Arewa

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Bindige Kansila Har Lahira A Jihar Arewa

  • Wasu yan bindiga sun kashe Saleh Yakubu, kansila mai jagorantar mazabar Allawa a karamar hukumar Shiroro na jihar Neja a safiyar ranar Juma'a
  • Rahotanni sun nuna cewa yan bindigan sun tare Yakubu ne tare da wan takwararsa yayin da suke kan babur a hanyarsu ta zuwa Allawa, suka umurci su sauka kuma suka bindige su
  • Emmanuel Umar, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja da Daniel Jagaba, shugaban ma'aikatan fadar ciyaman din karamar hukumar Shiroro, sun tabbatar da lamarin

Jihar Neja - Yan ta'adda sun bindige Saleh Yakubu, kansila mai shugabantar mazabar Allawa a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, har lahira, rahoton The Cable.

A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, Mr Emmanuel Umar, kwamishinan tsaron cikin gida da jin kan al'umma, ya ce lamarin ya faru a safiyar ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Tafi Har Fada Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Daya A Arewa, Sun Kashe Mutum Daya

Taswirar Neja
Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Bindige Kansila Har Lahira A Jihar Arewa. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Umar ya ce ya samu bayanai cewa an kashe kansilar yayin da ya ke dawowa daga Kuta, hedkwatar Shiroro zuwa Allawa, kauyensu.

Ya ce kansilar na kan babur ne tare da wani mutum a lokacin da aka kai musu harin.

Kwamishinan ya kara da cewa yan bindigan sun umurci kansilar da takwararsa su sako daga kan babur din sannan suka bindige su.

Daniel Jagaba, shugaban ma'aikatan fadar ciyaman din karamar hukumar Shiroro, yayin tabbatar da lamarin ya ce shima ya samu kira daga ciyaman ya kuma sanar da shi.

Martanin yan sandan jihar Neja kan kisar kansila

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar neja, Wasiu Abiodun, ya ce bai riga ya samu rahoto kan lamarin ba.

Allawa na daya cikin kauyukan da ke karamar hukumar Shiroro inda yan bindiga suke yawan kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Jiga-Jigan Jam'iyar APC Mai Mulki

Mutane da dama a garuruwan da ke karamar hukumar Shiroro sun mutu, ko suna tsare ko sun rasa muhallinsu sakamakon hare-haren yan bindiga.

Yan ta'adda sun kashe basarake, sun sace wasu mutum uku a jihar Neja

A wani rahoton, 'yan fashin daji sun kai hari karamar Mashegu na jihar Neja sun halaka magajin garin kauyen Mulo, sun kuma sace wasu mutane uku.

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, yan bindigan sun halaka Alhaji Usman Garba, sannan suka jefar da gawarsa a titi suka sace wasu mutum uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel