Jos
Gwamnan jihar Filato ya yi zama da sojoji, 'yan sanda da shugabannin kananan hukumomi kan kashe kashe da ake fama da shi a jihar. Ya ce za su hana kai hare hare.
'Yan ta'adda sun kai hari karamar hukumar Bassa a jihar Filato, sun kashe mutane 40. Kiristocin jihar sun fara shirye shiryen yin zanga zanga saboda kashe kashe.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar shugaban gudanarwa na kungiyar JIBWIS da ke da hedikwata a Jos reshen jihar Adamawa, Alhaji Muhammad Aliyu Kaka.
Kungiyar Izala ta yi sababbin nade nade. Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nada Malam Dalhatu Abubakar Hakimi a gurbin marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir.
Gwamnan Filato, Caleb Muftwang ya bayyana cewa mutanensa suna cikin mawuyacin hali yayin da fitinannun 'yan bindiga suka mamaye garurwa akalla 64.
Mashawarcin shugaban kasa, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa dole ne a samu hadin kan jama'a idan har za a yaki matsalar rashin tsaro da gaske a jihar Filato.
Babbar kotu da ke zamanta a Jos din jihar Plateau ta dage shari’ar kisan gilla kan Manjo-Janar Idris Alkali zuwa 28 da 29 ga watan Mayun shekarar 2025.
Wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga munanan hare-haren da yan bindiga suka kai a yankin Bokkos sun ba da labarin yadda lamarin ya faru ba zato ba tsammani.
Wata gagarumar iska da ta biyo bayan mamakon ruwan sama a jihar Filato ta rigurguza gidaje da rumbunan abinci sama da 70 a karamar hukumar Langtang ta Kudu.
Jos
Samu kari