Kasar waje
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya bayyana cewa sun yi tatttaunawa da Iran da kyakkyawar niyya, kuma sun gabatar da tayi mafi kyau a Pakistan.
Wata majiya da ke kusa da tawagar Iran a birnin Islamabad na Pakistan ta ce amincewar da Amurka ta yi na sakin wasu kadarorin Iran sun karawa kasar kwarin gwiwa.
A labarin nan, za a ji cewa kasar Iran da ke zaman sulhu da Amurka a Islamabad ta ja kunnen Trump a kan duk wani yunkuri na bi ta mashigar Hormuz da karfi.
Rahotanni daga birnin Islamabad na kasar Pakistan sun nuna cewa an kammala matakin farko na tattaunawa tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaba Trump ya sanar da cewa Amurka ta fara kwashe nakiyoyin da Iran ta dasa a mashigar Hormuz yayin da aka fara tattaunawar zaman lafiya a Pakistan.
Tawagar Amurka da ta Iran sun fara tattaunawa domin duba hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da zaman lafiya da kawo karshen yakin da duka jima suna yi.
Ismail Omar Guelleh da ya shafe shekaru yana mulki tun 1999 ya lashe zabe karo na 6 a jere. hukumar zabe ta kasar ta ce Ismail Guelleh ya samu mafi yawan kuri'u.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa idan har tattaunawar sulhu ba ta yu nasara ba, ya shirya sake kai hari kasar Musulunci ta Iran.
'Yar majalisar Amurka Yassamin Ansari ta yi wa Donald Trump wankin babban bargo, inda ta kira shi da mutum mai matsalar kwakwalwa kan yaki da Iran.
Kasar waje
Samu kari