Kotun Kostamare
Kotun sauraron kararrakin zabe ta tsige dan majalisar jam’iyyar PDP, Destiny Enabulele, wanda ke wakiltar mazabar Ovia ta kudu maso yamma a jihar Edo.
Majalisar Dattawa a yau Laraba 25 ga watan Oktoba ta rantsar da Amos Yohanna na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya maye gurbin Sanata Elisha Abbo na jam'iyyar APC.
Kotu ta jefa wani magidanci mai suna Gambo Adamu a magarkama bayan ya damfari surukarsa kudi naira miliyan 5 da nufin kulla aurenta da tsohon shugaban kasa Buhari.
Wata kotu a Minna, jihar Neja, ta yanke wa wasu matasa biyar hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari bayan ta kama su da laifin tono kan wani mutum don kudin asiri.
Alkalin wata kotun shari'ar musulunci dake zamanta a yankin Kwana hudu a jihar Kano ya yanke hukuncin yiwa wani Yakubu Haruna bulala 15, kan satar rake.
Wasu lauyoyi sun bai wa hamata iska bayan sun doku tare da fadan bakaken maganganu ga juna a cikin kotun majistare da ke jihar Enugu yayin zaman kotu.
LPPC ta fitar da sunayen duka manyan Lauyoyi 58 da su ka zama SAN, daga ciki akwai Emmanuel Moses Enoidem, Kehinde Olufemi Aina, Nghozi Oleh, Aaron Chile Okoroma.
David Yusuf, wani malamin makarantar sakandiren mata a babban birnin tarayya Abuja ya wati gari a gidan yari bisa tuhumar lakaɗa wa daibarsa dukan tsiya.
Wata kotu da ke Amurka ta daure magidanci daurin shekaru biyu a gidan kaso kan zargin cin zarafin wata mata, an ci tarar Jawad Ansari Dala dubu 40.
Kotun Kostamare
Samu kari