Namiji ko Mace: Bobrisky Ya Bayyana Ainihin Jinsinsa a Gaban Alkali

Namiji ko Mace: Bobrisky Ya Bayyana Ainihin Jinsinsa a Gaban Alkali

  • Shahararren dan daudu mai suna Idris Okuneye, da aka fi sani da Bobrisky, ya amsa cewa shi namiji ne yau Jumu'a, 12 ga watan Afrilu
  • Ya amsa hakan ne a lokacin da mai shari'a Abimbola Awogboro ya tambayesa jinsinsa kafin yanke masa hukuncin bisa zarginsa da wulakanta takardun naira
  • Bobrisky dai ya shahara da ikirarin cewa shi mace ce har ma yana cewa yana da mahaifa kuma a shire yake ya haihu.

Jihar Lagos - An wani yanayi mai kama da mafarki a yau Juma'a Idris Okuneye, fitaccen dan daudun da aka fi sani da Bobrisky, ya furta cewa shi namiji ne.

Ya furta hakan ne a gaban alkali a lokacin da ake shirin yanke masa hukunci bayan zarginsa da wulakanta takardun kudin Najeriya.

Bobrisky
Bobrisky ya tabbatarwa alkali cewa shi namij ne a lokacin yanke masa hukunci. Hoto: Bobrisky Asali: Facebook
Asali: Instagram

Bobrisky: Ikirarin zama mace

Kara karanta wannan

"Ya ki ya sumbace ta": Ango ya kunyatar da amaryarsa a gaban jama'a a wajen daurin aure

Dan daudun ya shahara da cewa shi mace ce har ma yana ikirarin cewa a shirye yake ya haifi ɗa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A mafiya yawan lokuta yakan sanya kaya ne na mata, yana kuma maƙe murya da tafiya irinta mata har ma da ikirarin cewa yana da saurayi.

Amma lokaci zuwa lokaci ya kan yi sutura a matsayin namiji. A bara lokacin da mahaifinsa ya rasu, Bobrisky ya halarci jana’izar a yankin Ijebu Igbo da ke jihar Ogun a matsayinsa na namiji.

Tambayar da alkali yayi wa Bobrisky

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kafin a yanke masa hukuncin, mai shari’a Abimbola Awogboro ya tambayesa jinsinsa, kuma cikin sauri ya amsa da cewa, “Ni namiji ne, mai Shari'a.”

An tura Bobrisky gidan gyaran hali

Hukumar EFFC ta wallafa a shafinta na Facebook cewa yau ne mai Shari'a Abimbola Awogboro ya yankewa Bobrisky hukunci bisa zargin wulakanta takardun kudi.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Bayan gabatar masa da zargin, ya amsa laifin ba tare da gardama ba. kuma duk da cewa ya nemi afuwa amma hakan bai kubutar da shi daga shan dauri ba.

Alkalin ya tura shi gidan gyaran hali kuma ya yanke hukuncin cewa zaman gidan yari ya fara ne daga ranar da aka kama shi.

Hukuncin yayi nuni da cewa Bobrisky zai zauna gidan gyaran hali na wata shida ba tare da tara ko beli ba.

Hukumar EFCC ta cafke Bobrisky

A wani rahoton kuma kun ji cewa, hukumar EFCC a jihar Legas ta kama fitaccen dan daudu a Najeriya, Idris Okuneye a daren Laraba, 3 ga watan Afrilu.

Hukumar ta dauki matakin ne bayan zargin Bobrisky da watsa takardun naira da kuma cin mutuncinta wanda ta sabawa doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel