Kano: Kotu Ta Sake Daukar Mataki Kan ’Yar TikTok, Murja Kunya, Ta Fadi Dalilai

Kano: Kotu Ta Sake Daukar Mataki Kan ’Yar TikTok, Murja Kunya, Ta Fadi Dalilai

  • Yayin da ake ci gaba da shari'ar Murja Ibrahim Kunja, babbar kotu a jihar Kano ta ba da belinta kan kudi N500,000
  • Kotun ta kuma umarci ba ta rahoton binciken lafiyar kwakwalwar matashiyar 'yar TikTok din da ake zargi
  • Alkalin Murja, Yusuf Ali Faragai shi ya bukaci ba wacce ya ke karewa beli a wata kotu inda ya ce laifinta ya cancanci ba ta beli

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotu a jihar Kano ta ba matashiyar 'yar TikTok, Murja Kunya beli kan kudi N500,000.

Kotun ta ba da belin ne da sharadin kawo mutum biyu da za su tsaya mata wanda daya dole zai kasance na kusa da ita, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Abacha ya karkatar da maƙudan kudi a mulkinsa? Buba Galadima ya fayyace gaskiya

Kotu ta yanke hukunci kan Murja a jihar Kano
Kotu ta ba da belin Murja Kunya kan kudi N500,000 a jihar Kano.
Asali: Facebook

Wane mataki kotun ta dauka a Kano?

Alkalin kotun, Nasiru Saminu ya ba hukumar kula da asibitocin jihar da kuma asibitin Dawanau umarnin ba kotu rahotonsu da suka kammala kan wacce ake zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan kotun shari'ar Musulunci ta ba da umarnin tsare ta tare da duba lafiyar kwakwalwarta, cewar Leadership.

Wace bukata lauyan Murja ya ke so?

Lauyan wacce ake kara, Yusuf Ali Faragai shi ya bukaci belin a wata kotu inda ya ce laifin da ta aikata ya na bukatar beli.

Yusuf ya kuma bukaci ganin wacce ya ke karewa domin sanin halin da take ciki domin kawo ta gaban kotun.

Wadanda su ke cikin shari'ar akwai kwamishinan Shari'a na jihar Kano da hukumar Hisbah da kuma kotun shari'ar Musulunci da ke Kwana Hudu.

Kara karanta wannan

N6bn: 'Yan APC a Kano sun taso Gwamna Abba a gaba kan kudaden ciyar da bayin Allah a Ramadana

Yan sanda sun bukaci diyya daga Murja

A baya, mun ruwaito muku cewa rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta kai korafi kan matashiyar 'yar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya.

Rundunar ta bukaci biyan diyya daga Murja har na N500,000 saboda neman bata mata suna da matashiyar ta yi yayin da ake Shari'ar.

'Yan sandan sun zargi Kunya da maka su a gaban kotu ba tare da sanin ainihin abin da suka aikata ba sa suka cancanci haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel