Kotun Kostamare
Babbar kotun tarayya ta umarci alkalan Kano guda biyu da su ajiye mukaman da gwamnatin Kano ta ba su na bincikar tsohon gwamna Abdullahi Ganduje.
A yau ne babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki ta ci gaba da sauraron shari'ar matashin da ya kashe mutane 23 a karamar hukumar Gezawa a Kano.
Yayin da rikicin masarauta ke kara kamari a Sokoto, babbar kotun jiha ta dakatar da gwamna Ahmed Aliyu daga tsige hakimai biyu da ta dakatar a baya.
Mutuwar Mai shari’a Adegboye Gbolagunte na babbar kotun jihar Oyo, ta kawo cikas ga ci gaba da shari’a da dama a galibin kotunan jihar a ranar Talata.
Wata kotu da ke zamanta a Abeokuta ta kama wani matashi mai shekaru 35, Kabiru Lawal da laifin zambar rago da tumaki sannan ya cefanar da su ya kalmashe kudin.
Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a filin hockey a jihar Kano ta fusata tare da tura wani magidanci gidan yari bayan an zarge shi da dukan matarsa.
Kotun Majistare da ke birnin Osogbo a jihar Osun ta daure tsohon shugaban karamar hukuma, Mista Tajudden Babatunde shekaru hudu a gidan gyaran hali.
Babbar mai shari’a ta Kano, Dije Abdu Aboki ya ta bayyana cewa atsalandan a bangaren shari’a yana hana yanke hukunci da rashin gaskiya da adalci.
Kotu ta sanya ranar 4 ga watan Yuli domin sauraren karar da aka shigar kan Shafi’u Abubakar, bisa zarginsa da kona wani masallaci a Kano tare da kashe mutane 19.
Kotun Kostamare
Samu kari