Kano: Fitacciyar Ƴar TikTok, Murja Kunya, Ta Shigar da Sabuwar Buƙata a Babbar Kotun Tarayya

Kano: Fitacciyar Ƴar TikTok, Murja Kunya, Ta Shigar da Sabuwar Buƙata a Babbar Kotun Tarayya

  • Murja Kunya, fitacciyar ƴar TikTok ɗin nan ta garzaya gaban babbar kotun tarayya mai zama a jihar Kano tana neman beli
  • Lauyanta, Barista Yusuf Ali Faragai, ya buƙaci kotun ta ba da belin Murja saboda laifin da ake tuhumarta da shi yana da beli
  • Sai dai ɓangaren gwamnati ta yi fatali da buƙatar kuma daga bisani alkalin kotun ya ɗage zaman zuwa ranar 28 ga watan Maris domin yanke hukunci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Fitacciyar ƴar TikTok ɗin nan ta jihar Kano, Murja Ibrahim Kunya, ta shigar da ƙarar neman beli a gaban babbar kotun tarayya mai zama a jihar Kano.

Idan ba ku manta ba babbar kotun shari'ar addinin Musulunci ta umarci a ci gaba da tsare ta a gidan gyaran hali kuma a mata gwajin kwaƙwalwa domin tabbatar da lafiyarta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko da sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga a watan Azumi

Murja Kunya.
Murja Kunya ta shigar da buƙata a babbar kotun tarayya Hoto: Murja Kunya
Asali: Facebook

Mai shari'a Nasiru Saminu na kotun shari'a ya ƙi amincewa da bukatar neman belin da ta shigar gabansa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Murja Kunya ta nemi beli?

Amma lauyan da ke kare Murja Kunya, Barista Yusuf Ali Faragai, ya shigar da ɓukatar belinta a babbar kotun tarayya, yana mai cewa laifin da ake zarginta yana da beli.

Lauyan ya kuma buƙaci sanin wurin da ake tsare da wanda yake karewa daga bakin waɗanda yake kara domin kula da lafiyarta, Tribune Online ta tattaro.

Ya kuma buƙaci waɗanda suka gurfanar da Murja Kunya su kawo ta gaban kotu a zaman shari'ar da ake ci gaba da yi.

Lauyan fitacciyar ƴar TikTok ɗin ya jero waɗanda yake ƙara da suka haɗa da Antoni Janar na jihar Kano, rundunar Hisbah da kotun shari'ar Musulunci ta Kano da ke Kwana Huɗu.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

Kotu za ta yanke hukunci

Sai dai Lauyan waɗanda ake kara, Barista H.H Suleiman, ya nuna rashin amincewa da bukatar.

Barista Suleiman ya yi musun cewa ƙarar cin mutunci ne ga tsarin shari'a saboda an riga da an shigar da irinta a gaban babbar kotu.

Bayan sauraron bayanai daga kowane bangare, mai shari'a Abdullahi M Liman, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga watan Maris domin yanke hukunci.

Ƴan sanda sun nemi Murja ta biya diyya

A wani rahoton kun ji cewa Rundunar ’yan sanda a jihar Kano ta bukaci fitacciyar 'yar TikTok , Murja Ibrahim Kunya da ta biya ta diyyar N500,000.

Rundunar ta shigar da korafin ne gaban babbar kotun jihar Kano inda ta bukaci a cire sunanta a cikin wadanda ake kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel