Kano: Kotu Ta Sake Daukar Mataki Kan Shari’ar Hafsat ‘Chuchu’ da Ake Zargi da Kisan Nafiu

Kano: Kotu Ta Sake Daukar Mataki Kan Shari’ar Hafsat ‘Chuchu’ da Ake Zargi da Kisan Nafiu

  • Yayin da ake ci gaba da shari’ar Hafsat 'Chuchu' da Nafiu Hafizu, kotun da ke zamanta a Kano ta sake ba da umarnin duba kwakwalwarta
  • Kotun da ke kan hanyar Miller ta umarci sake duba lafiyar kwakwalwar Hafsat da ake zargin ta hallaka saurayinta shekarar da ta wuce
  • Wannan na zuwa ne bayan asibitin masu tabin kwakwalwa ta Dawanau ta mika rahoto kan gwajin da suka yi a shari’ar da aka yi a baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar kotu da ke zamanta a jihar Kano ta ba da umarnin sake gwajin kwakwalwa ga Hafsat 'Chuchu' wacce ake zargi da kisan saurayinta.

Kara karanta wannan

An garkame fursunoni 300 a gidan yarin Kano ba tare da aikata laifin komai ba, in ji ‘yan sanda

Kotun ta umarci duba lafiyar kwakwalwarta a asibitin mahaukata karkashin kulawar gidan gyaran hali na Kurmawa.

Kotu a Kano ta sake daukar mataki kan shari'ar Hafsat 'Chuchu' da Nafiu
Kotun ta sake umartar duba lafiyar kwakwalwar Hafsat da ake zargi da kisan kai. Hoto: Nafiu Hafizu, Hafsat 'Chuchu'.
Asali: Facebook

Wane umarni kotun ta bayan kan Hafsat 'Chuchu'?

Idan ba a manta ba asibitin masu tabin kwakwalwa ta Dawanau ta mika rahoto kan gwajin da suka yi a zaman shari’ar da aka yi a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wacce ake zargin, Hafsat 'Chuhcu' da ke rayuwa a Unguwa Uku ta na fuskantar tuhuma kan zargin kisan kai da ya shafi wani mai aiki a gidanta.

Mai Shari’a, Zuwaira Yusuf ta umarci likitoci su sake duba Hafsat don ba da rahoto da sakamako da za a yi hukunci a kai, cewar Daily Trust.

Kotun ta yi fatali da ba da belinsu

Har ila yau, kotun ta ki amincewa da ba da belin mijin Hafsat mai suna Dayyabu Abdullahi da kuma Adamu Muhammad da Nasidi Muhammad kan zargin ba da bayanan karya.

Kara karanta wannan

Daurawa: Ana tsaka da sulhu tsakanin Abba da Hisbah, hukumar ta samu babbar nasara

Zuwaira Yusuf ta ce laifukan da ake zarginsu masu girma ne don haka basu bukatar beli har sai idan akwai wani dalili mai karfi.

Lauyoyin wadanda ake zargin sun bukaci kotun ta dage ci gaba sauraran karar kasa da kwanaki 14 karkashin sashe na 390.

Daga bisani alkalin kotun ta dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar 26 ga watan Maris, rahoton The Eagle.

Kotu ta tsare Hafsat ‘Chuchu’

Kun ji cewa kotu ta ba da umarnin ci gaba a tsare Hafsat Surajo da ake zarginta da kisan saurayinta a jihar Kano.

Wacce ake zargin an tsare ta ne bayan zargin kisan Nafiu Hafizu mai shekaru 38 har lahira kan wasu zarge-zarge a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel