Abuja
Ministan tsare-tsaren kasafin kudi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya fadi yadda Muhammadu Buhari ya rayu da tawali’u da gaskiya, kuma ya goyi bayan kawo sauyi.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida shugaban Bankin Noma tare da wasu mutane takwas a hukumomin tarayya domin farfaɗo da shugabanci.
Bayan karrama marigayi Muhammadu Buhari da Bola Tinubu ya yi, jikan tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari ya ce kakansa bai samu haka daga gwamnati ba a 2018.
Gwamnatin tarayya ta gargadi jihohi 11 kan ambaliya daga 16-20 Yuli, ta kuma kafa shirin inshora don dakile barazanar da ambaliya ke haddasawa a kasa.
Ɗan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Yusuf ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa mutunta mahaifinsa da jana’iza ta kasa da aka shirya saboda shi.
NiMet ta ce za a yi ruwan sama da tsawa a Arewa ranar Alhamis, 17 ga Yuli, 2025; sauran yankuna za su sami ruwa kaɗan, kuma an shawarci jama'a su yi taka tsantsan.
Bayan ya yi magana kan ingancin kiwon lafiya a Najeriya, manyan likitoci sun ca caccake Femi Sarakuna inda da cewa akwai kwararru sosai a kasar da za su ba da kulawa
Fadar shugaban kasa za ta shirya taron FEC domin girmama Muhammadu Buhari da ya rasu. Za a yi wa Buhari addu'a a masallacin Abuja da coci ranar Lahadi.
Sanata mai wakiltar Abuja a a Majalisar Dattawa, Ireti Kingibe ta bayyana cewa a iya hangenta, babban kuskuren Shugaba Bola Tinubu shi ne naɗa Nyesom Wike.
Abuja
Samu kari