Zamfara: Tsohon Sanata Ya Fadi Hanyar Kawo Karshen Matsalar Tsaro Har Abada

Zamfara: Tsohon Sanata Ya Fadi Hanyar Kawo Karshen Matsalar Tsaro Har Abada

  • Yayin da ake fama da matsalar tsaro a Najeriya, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana hanyoyin kawo karshen wannan annoba
  • Sanata Marafa ya ce ba tare da bambancin addini ko kabilanci ba, ya kamata a dukufa wurin yin addu'o'i da kuma hadin kai a kasar
  • Sanatan ya bayyana haka ne a jiya Talata 19 ga watan Maris inda ya bukaci Musulmai su dage da addu'a a wannan wata mai albarka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Tsohon Sanata a jihar Zamfara, Kabiru Marafa ya bayyana hanyar dakile matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Sanata Marafa ya ce hanya daya mafi sauki domin dakile matsalar ita ce addu'a da kuma hadin kai daga 'yan kasar, a cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Wasu ma'aikata za su samu karin albashi, Tinubu ya aika takarda zuwa ga Majalisar Tarayya

Tsohon sanata ya kawo mafita kan matsalar tsaro a Najeriya
Sanata Kabiru Marafa ya ce addu'o'i da hadin kai ne kadai za su kawo karshen matsalolin Najeriya. Hoto: Kabiru Marafa.
Asali: Twitter

Marafa ya kawo mafita kan matsalar tsaro

Ya ce wannan hadin kai da addu'a ana bukatarsu ne daga dukkan 'yan kasar ba tare da bambancin addini ko kabilanci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marafa wanda ya wakilci mazabar Zamfara ta Tsakiya daga shekarar 2011 zuwa 2019 ya bayyana haka a jiya Talata 19 ga watan Maris.

Ya ce matsalar tsaron za ta kawo karshe idan har 'yan kasar suka hada kai ba tare da nuna bambanci a tsakani ba, cewar Head Topics.

Marafa ya roki al'ummar Musulmi a Ramadan

Ya kuma bukaci al'ummar Musulmai da su yi amfani da wannan watan Azumi domin yin addu'a ga ci gaban kasar.

"A yayin da mu ke fama da matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki, ya kamata mu hada kai domin kawo karshen matsalolin."
"Ba tare da bambancin addini ba, yanzu lokaci ne da ya kamata mu hada kai tare da yin addu'o'i domin ci gaban kasar."

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da sabon umarni ga rundunar tsaro bayan kisan sojoji 16, ya yi Allah wadai

"A wannan wata na Ramadan, ya kamata mu kara kaimi wurin yin addu'a domin samun kwanciyar hankali da kuma ci gaban Najeriya."

- Kabiru Marafa

'Yan banga sun hallaka malamin Musulunci

A baya, mun ruwaito muku cewa wasu da ake zargin 'yan banga ne sun hallaka wani fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Zamfara.

Marigayin mai suna Mallam Abubakar Hassan Mada ya gamu da ajalinsa ne bayan 'yan sa kai din sun dauke shi daga gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel