Abacha Ya Karkatar da Maƙudan Kudi a Mulkinsa? Buba Galadima Ya Fayyace Gaskiya

Abacha Ya Karkatar da Maƙudan Kudi a Mulkinsa? Buba Galadima Ya Fayyace Gaskiya

  • Yayin da ake ta zargin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha kan satar kudi, jigon NNPP, Buba Galadima ya fayyace komai
  • Galadima ya ce ya na cikin gwamnatin inda ya tabbatar da cewa ko sisin kwabo tsohon shugaban kasar bai dauka ba a lokacinsa
  • Ya kara da cewa har yanzu a tunaninsa babu nagartaccen shugaban kasa kamar Abacha saboda abubuwan ya da kawo kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa ba a taba samun nagartaccen shugaban kasa kamar Janar Sani Abacha ba.

Galadima wanda tsohon na hannun daman Muhammadu Buhari ne ya ce Abacha ko sisin kwabo bai dauka ba lokacin da ya ke mulki.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya karyata masu jita-jita cewa ya ware N6bn don ciyar da Kanawa a Ramadana

Buba Galadima ya fadi irin ayyukan da Sani Abacha ya yi a Najeriya
Buba Galadima ya ce ba a taɓa samun nagartaccen shugaban kasa irin Sani Abacha ba. Hoto: Buba Galadima, Sani Abacha.
Asali: Facebook

Galadima ya ce babu kamar Abacha

Buba ya bayyana haka ne yayin hira a cikin wani faifan bidiyo da Tribune ta yada a yau Lahadi 24 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tun da ake shugabannin soji na kasar Najeriya, Abacha har yanzu shi ne mafi nagarta da kasar ta yi a tarihi.

Ya kara da cewa Abacha ya yi abin a zo a gani inda ya ce a cikin shekaru hudu da ya yi darajar naira zuwa dala ba ta wuce N84 ba.

Har ila yau, Galadima ya ce a zamanin Abacha ne farashin fetur bai taba sauyawa ba bayan ayyukan raya kasa da ya yi.

Ayyukan da Abacha ya yi - Buba Galadima

“A wuri na Abacha shi ne mafi kyawun shugaban kasa da aka taba yi wanda ya gina sakatariyar Tarayya da Majalisar Tarayya da sauran ayyuka.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya roki 'yan Najeriya hanya 1 da za su inganta darajar naira da kansu cikin sauki

“A cikin shekaru hudu da ya yi, dala ana siyar da ita ne N84 kuma farashin fetur bai taba sauyawa ba.”
“Wani shugaban ne zai bugi kirji ya ce farashin dala ya tsaya a wuri daya har watanni shida?, sannan ko sisin kwabo Abcha bai dauka ba saboda ina cikin gwamnatin.”

- Buba Galadima

Yadda Buhari ya so ceton Nyako

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi kokarin janye karar da ake yi kan tsohon gwamnan Adamawa, Murtala Nyako.

Tsohon lauyan Nyako ne ya bayyana haka bayan an sake gurfanar da Nyako a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel