Badaƙalar N109bn: EFCC Ta Yi Martani a Kan Zargin Ƙulla Wa Tsohon Minista Makirci

Badaƙalar N109bn: EFCC Ta Yi Martani a Kan Zargin Ƙulla Wa Tsohon Minista Makirci

  • Hukumar EFCC ta ƙaryata zargin da tsohon Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris ya yi na cewa an hada baki da shi don kullawa wani sharri
  • Jami'in hukumar, Mahmud Tukur, ya shaidawa kotun tarayya da ke Abuja cewa, hukumar ba ta da wani nufi na kulla wa tsohuwar ministar kuɗi sharri
  • Wannan na zuwa ne bayan da Idris, wanda EFCC ke tuhuma da laifuffuka 14, ya yi korafin cewa hukumar ta tursasashi rubuta jawaban ƙarya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani dan jami'i a hukumar EFCC, Mahmud Tukur, ya musanta cewa ya bukaci tsohon Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris da ya saka sunan tsohuwar ministar kuɗi da wasu a tuhumar da ake yi masa.

Kara karanta wannan

An kama mutumin da ya yi barazanar kashe shugaban EFCC na ƙasa, ya faɗi gaskiya

EFCC ta musanta zargin ƙulla wa tsohon minista sharri
Jami'in EFCC ya ce babu inda suka tursasa Idris ya rubuta jawaban ƙarya. Hoto: @FOdorige
Asali: Facebook

Tukur ya ce zargin cewa ya yi wa Idris alkawarin yi masa sassauci idan ya ja wa tsohuwar ministar kuɗi da sauran su sharri, “karya ce tsagwaronta”.

Da yake jawabi yayin zaman shari’ar kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Tukur ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ban taba yi masa alkawarin cewa ba za a tuhume shi ba.
"Babu wani daga cikin hukumar mu da ya kulla wata yarjejeniya ko hada baki da wanda ake kara."

Tuhumar da EFCC take yi wa Idris

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, an gurfanar da Idris da wasu mutane biyu da kamfani daya a gaban kotu bisa laifuffuka 14 da suka hada da sata da kuma zamba cikin aminci da ya kai N109.5bn.

Mutanen da kamfanin su ne; Godfrey Akindele, Mohammed Kudu Usman, da kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

Kotun ta bayar da umarnin a yi 'shari’a cikin shari’a' biyo bayan korafin da lauyan Idris, Chris Uche (SAN) ya gabatar na cewa wanda yake karewa bai yi jawabansa ga EFCC bisa radin kansa ba.

Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, Idris ya yi ikirarin cewa EFCC ta yaudare shi inda ya amince da sa hannu a badakalar naira biliyan 109.4.

EFCC: "Ba mu tursasa shi ba" - Tukur

Bisa jagorancin lauyan EFCC, Oluwaleke Atolagbe, Tukur ya jaddada wa kotun cewa dukkanin jawabai 13 da wadanda ake karar suka yi babu tursasawa a ciki.

Ya kara da cewa hukumar ta yi wa tsohon akawun tarayyar tambayoyi a gaban lauyansa, kuma babu wanda ya cusa masa magana a bakinsa.

Alkalin kotun, Mai shari'a Yusuf Halilu ya dage sauraron karar har zuwa ranar 15 ga watan Mayu.

Yarjejeniyar EFCC da Ahmed Idris

Kara karanta wannan

Okuama: Shugaban majalisar dattawa ya faɗi waɗanda yake tunanin suna da hannu a kisan sojoji 17

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris ya ce hukumar EFCC ta nemi ya hada hannu da ita wajen tsoma tsohuwar ministar kuɗi a badaƙalar N10.9.4bn.

Idris ya ce dukkanin jawaban da hukumar ta gabatar a gaban kotu da sunan shi ya su ba gaskiya ba ne, a cewar sa, EFCC ta tursasa shi fadin kalaman da bai yi ra'ayi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel