Jihar Kano
Hukumar tsaron farar hula ta NSCDC ta tabbatar da cafke masu safarar man fetur daga jihar zuwa Katsina.Ta kama litar mai dubu ashirin, kuma ta mayar da su gidan mai.
Rundunar 'yan sanda a Kano ta sanar da cafkewa tare da gurfanar da masu manyan laifuka 3000 cikin shekara guda. Kwamishinan yan sandan jihar ne ya bayyana hakan.
Wata dalibar aji uku a jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Aisha Yahaya ta rigamu gidan gaskiya. An tsinci gawar wata dalibar a dakinta.
Kwamnadan Hisba na jihar Kano sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun sake sababbin tsare-tsare kan shirin auren zawarawa inda za a saka bangarori da dama.
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sanya dokar ta baci a harkar ilimi. Kwamishinan ilimi na jihar ne ya yi bayanin ranar Litinin da ta wuce a jihar Jigawa
An shiga jimami bayan wasu dalibai guda biyu sun gamu da ajalinsu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Kano a hanyarsu ta komawa kwalejin aikin gona ta Audu Bako.
Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Salihu Lukman, ya bayysna dalilin da ya sanya gwamnatin jihar Kano ta samu nasarar yi wa Ganduje illa a siyasance.
Mai Shari'a, Farouk Adamu, shugaban kwamitin binciken shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya ce za su yi duba na musamman kan zargin badakalar da aka tafka.
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa dokar gwajin lafiya kafin aure a fadin jihar. A jiya Litinin ne majalisar ta gama karanta kudurin dokar
Jihar Kano
Samu kari