Portable Mai Wakar Zazu Ya Janyo Muhawara Yayin Da Ya Dora Hotunan Shanu 5 Da Raguna 2 Na Shagalin Sallah

Portable Mai Wakar Zazu Ya Janyo Muhawara Yayin Da Ya Dora Hotunan Shanu 5 Da Raguna 2 Na Shagalin Sallah

  • Shahararren mawaƙin nan na kudancin Najeriya, Portable, ya gama shiryawa tsaf domin gudanar da bukukuwan Sallah babba ta bana
  • Mawaƙin wanda ake kira da Zazu Zeh Crooner ya ɗora bidiyon shanu biyar da raguna biyu da ya saya gabanin bikin Sallah a kafar sada zumunta
  • A cewar Portable, ya sayi shanun da ragunan ne da kuɗinsa ba wai kyauta aka ba shi ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fitaccen mawakin nan na kudancin Najeriya, Portable, ya janyo muhawara a intanet bayan da ya bayyana shirye-shiryen da yake yi na bikin babbar sallah wato Eid-el-Kabir da ke ta ƙara ƙaratowa.

A Najeriya da ma wasu sassa daban-daban na duniya, za a gudanar da bukukuwan sallar ne a ranar Laraba, 28 ga watan Yuni da muke ciki.

Mawaki Portable ya janyo muhawara a Intanet
Mawaki Portable Zazu Zeh ya janyo Muhawara a Instagram bayan da ya dora bidiyon dabbobin da zai yi layya da su. Hoto: @Portablebaeby
Asali: Instagram

Takaitaccen bayani kan bikin babbar sallah

Kara karanta wannan

NSA: Sabon Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaron Kasa Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

Bikin babbar sallah ko Eid-el-Kabir biki ne na musamman na shekara-shekara ga Musulmai domi n girmama yadda Annabi Ibrahim (AS) ya yi ƙoƙarin sadaukar da ɗansa, Annabi Isma'il, bisa ga umarnin Allah.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Domin koyi da wannan umarni, Musulmai a wannan rana ta musamman, suna yanka raguna, shanu, rakuma, ko wasu dabbobin da suka halatta a yi layya da su.

Portable a bidiyon da ya wallafa, ya nuna cewa shi ma ya gama shiryawa tsaf, don gudanar da shagalin babbar sallah.

Portable ko Zasu Zeh Crooner, ya ɗora faifan bidiyon ne a shafinsa na Instagram, wanda yake nuni da shanun biyar da raguna biyu da ya saya gabanin sallar ta layya.

Ya bayyana cewa da kuɗinsa ya siyo shanun da ragunan ba wani ne ya ba shi su kyauta ba. Ya ce shekarar ta bana ta yi kyau sosai.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

Mawaƙi Zazu ya ƙara da cewa zai raba naman ne ga masallatai, sarakuna, iyayensa da ma har maƙiyansa. Duba bidiyon a nan ƙasa:

Masu amfani da kafafen sadarwa sun yi muhawara kan shanu 5 da raguna 2 da Portable ya siya na sallah

Wasu daga cikin masoyansa sun ji daɗin bidiyon shanu da ragunan da ya ɗora, a yayin da suka tofa albarkacin bakunansu. Karanta wasu daga cikin abubuwan da suka ce a ƙasa:

Olabarca20 ya ce:

"Yanzu wannan da magyazon san kake son yankawa, kaji tsoron Allah."

__pappyg ya ce:

"Lallai fa a wannan karan ina wajen Portable”

al_jami ya ce:

“Waɗannan shanun a ba su riƙa ba tukunna."

fine.boy_flames ya ce:

"Shin shanu biyar da raguna biyu ba su yi yawa ba?"

k.jones_official ya ce:

"Wannan ai ɗan magyazon sa ne."

Shugaba Tinubu ya sanar da ranakun hutun sallar bana

Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a baya kan hutun bukukuwan babbar sallah ta bana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar.

Kara karanta wannan

"Ya Daina Nuna Mun Soyayya" Wata Mata Ta Roki Kotu Ta Raba Auren Kuma Ta Umarci Mijin Ya Riƙa Biyanta N30,000

Shugaba Tinubu ya bayyana ranakun Laraba, 28 ga watan Yuni, da Alhamis 29 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutun na babbar sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel