Babangida: PDP ta amince da dakatarwar da aka yi wa daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya a Arewa

Babangida: PDP ta amince da dakatarwar da aka yi wa daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya a Arewa

- PDP ta ce Muazu Babangida Aliyu ya taimakawa APC da kudi a zaben 2015

- A dalilin haka ne aka tabbatar da dakatar da tsohon Gwamnan daga jam’iyya

- Jam’iyyar PDP ta maye gurbin Aliyu da Nuhu Zagbayi a matsayin Jagoranta

Jaridar Daily Trust ta ce jam’iyyar PDP ta reshen jihar Neja, ta tabbatar da cewa Mu’azu Babangida Aliyu ya na nan a matsayin wanda aka dakatar.

Jam’iyyar PDP ta ce an dakatar da tsohon gwamna, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu saboda rawan da ya taka wajen juya wa Goodluck Jonathan baya a 2015.

Rahoton ya ce PDP ta fito, ta bada wannan sanarwa ta bakin mai magana da yawun bakinta a mazabar tsohon gwamnan, Malam Yahaya Mohammed Usman.

KU KARANTA: PDP ta dakatar da tsohon Gwamna Babangida Aliyu

Yahaya Mohammed Usman ya ce su na tare da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda ya ce Mu’azu Babangida Aliyu ya na bin PDP bashin neman afuwa.

“An wanke mu, mun fada wa ‘Yan Najeriya da mutanen jihar Neja cewa Dr. Aliyu ya yaudare mu, ya yi wa jam’iyyar APC aiki.” Inji Yahaya Mohammed Usman.

“Ya yaudari jam’iyya, da shugaban kasa (na wancan lokaci), Goodluck Jonathan da ‘dan takarar zabenmu na gwamnan jiha, Alhaji Umar Nasko.” Inji jam’iyyar.

Ya ce: “Mun fada cewa ya dauki kudi, ya ba jam’iyyar hamayya (a wancan lokacin) gudumuwa.”

KU KARANTA: Dalilin juyawa Goodluck Jonathan baya a zaben 2015 - Aliyu

PDP ta amince da dakatarwar da aka yi wa daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya a Arewa
Tsohon Gwamna, Dr. Babangida Aliyu
Asali: UGC

Kakakin jam’iyyar yake cewa: “Mun tabbatar da karin matsayin da aka yi wa Dr. Shem Nuhu Zagbayi a matsayin jagoran PDP a yankin da Dr. Aliyu ya fito.”

Mai magana da yawun bakin jam’iyyar hamayyar a Neja, bai iya bada wata hujja da za ta tabbatar da cewa Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ya ba APC kudi a 2015 ba.

Dr. Shem Nuhu Zagbayi ya taba rike mukamin mataimakin gwamna a jihar Neja a lokacin PDP.

A kwanakin baya kun ji yadda uwar-jam'iyya ta rusa dakatarwar da aka yi wa Jigon PDP, Muazu Babangida Aliyu saboda laifin yi wa Goodluck Jonathan zagon-kasa.

Shugabannin riko na yankin Arewa ta tsakiya sun yi watsi da matakin da reshen PDP na Neja ta dauka, su ka ce tsohon gwamnan ya na cikin 'yan majalisar BOT na PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel