Lambar El Rufai Ta Fito a Tuhumar da Ake Yi Wa Tsohon Jami'in Gwamnatin Kaduna

Lambar El Rufai Ta Fito a Tuhumar da Ake Yi Wa Tsohon Jami'in Gwamnatin Kaduna

  • Tsohon kwamishinan kuɗi a gwamnatin Nasir El-Rufai ya ba jami'an tsaro bayanai kan zargin da ake masa na almundahanar kuɗi
  • Alhaji Muhammad Bashir Sa'idu ya ambaci sunan tsohon gwamnan na Kaduna a bayanan da ya bayar ga jami'an tsaro
  • Tsohon shugaban ma'aikatan fadar.gwamnatin ya bayyana cewa ba shi ba ne ke da alhaki kan sauya kuɗaɗen gwamnati ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Muhammad Bashir Sa'idu tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati a lokacin mulkin Nasir El-Rufai, ya ba da bayanai kan tuhumar da ake yi masa ta almundahanar kuɗaɗe.

Ana zargin tsohon kwamishinan kuɗin ya ambaci sunan Nasir El-Rufai, a bayanan da ya bayar kan tuhumar da ake yi masa.

An ambaci sunan El-Rufai
Bashir Sa'idu ya ambaci sunan El-Rufai a tuhumar da ake yi masa Hoto: Nasir El-Rufai, Bashir Sa'idu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ce wata kotun majistare da ke Rigasa ta tura Alhaji Sa’idu zuwa gidan gyaran hali na Kaduna bayan jami’an tsaro sun kama shi tare da gurfanar da shi a ranar 31 ga watan Disamba, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gama sukar Tinubu, zai kashe N400m don sayen kwamfuta 6

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin tsohon jami'in gwamnatin El-Rufai

Ana zargin tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin da sayar da Dala miliyan 45 mallakin gwamnatin jihar Kaduna, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 18.45, a farashi mai rahusa na N410 kan kowace dala.

Hakan ya saɓawa farashin kasuwa na N498 kan kowace dala, wanda hakan ya janyo asarar Naira biliyan 3.96 ga gwamnatin jihar.

A cewar masu shigar da ƙara, laifin ya faru ne a shekarar 2022, lokacin da Alhaji Sa’idu ke matsayin kwamishinan kuɗi a gwamnatin El-Rufai.

Haka kuma, masu shigar da kara sun yi zargin cewa Naira biliyan 3.96 ɗin Alhaji Sa'idu ne ya yi sama da faɗi da ita, wanda hakan ya saɓawa sashe na 18 na dokar hana almundahanar kuɗi ta 2022.

Me Bashir Sa'idu ya ce kan El-Rufai?

Wani jami’in tsaro da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyanawa wasu manema labarai a Kaduna cewa Alhaji Sa’idu ya ambaci El-Rufai a cikin bayanan da ya bayar ga ƴan sanda.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi alakarsa da El-Rufai, ya magantu kan barinsa APC da hana shi Minista

Jami'in tsaron ya ce tsohon kwamishinan ya ce ba shi ba ne yake da alhakin sauya kuɗaɗe.

"Hanyar da ake bi wajen sauya kuɗi ba alhakin kwamishinan kuɗi ba ne, amma na mai girma gwamna ne a wancan lokacin, Malam Nasir El-Rufai."
"Duk lokacin da buƙatar sauya kuɗi zuwa naira ta taso, gwamna zai ba da umarnin adadin abin da za a sauya."
"Ana samun tayi daga masu buƙatar saye daban-daban, kuma a mafi yawan lokuta, tayin da na ke miƙawa mai girma gwamna don amincewa ya kan fi daraja kan wanda ke kasuwar canji."

- Alhaji Muhammad Bashir Sa'idu

Me doka ta tanada kan zargin?

Sashe na 18(3) na dokar hana almunhanar kuɗi ta 2022 ya tanadi cewa duk wanda ya karya sashe na (2) zai fuskanci hukunci na ɗaurin shekaru huɗu zuwa 14 a gidan yari.

Sashen ya kuma yi tanadin tara da ba za ta gaza ninki biyar na darajar kuɗaɗen da aka samu daga laifin ba, ko duka biyun.

Kara karanta wannan

Abin da ya hana gwamnoni taimakon Malam El Rufai lokacin da aka naɗa shi minista

El-Rufai ya ziyarci Bashir Sa'idu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya kai ziyara gidan gyaran hali ga Alhaji Muhammad Bashir Sa'idu.

Nasir El-Rufai ya ziyarci tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati a lokacinsa, ne bayan an tsare shi bisa zargin almundahanar kuɗi,

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng