Bikin cika shekara 61 da haihuwar Kwankwaso

Bikin cika shekara 61 da haihuwar Kwankwaso

Magoya bayan Sanata mai wakiltar jihar Kano ta Tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda shine tsohon gwamnan jihar Kano, sun hadu wajen gudanar da taro a Otel din Oriental dake gundumar Lekki a jihar Legas, domin taya shi murnar bikin cikar sa shekaru 61 da haihuwa.

Abokan hulɗa da Kwankwaso na jihar Legas da Yankin Kudu Maso Yamma sune suka halarci wannan taro tare da wakilai daga kungiyar daliban Najeriya ta NANS (National Association of Nigerian Students).

A cikin jawabin daya daga cikin wadanda suka shirya wannan taro Misis Fisher Thomas, ta bayyana cewa, an shirya wannan biki ne domin nuna ƙauna ga wannan mutumin daya zamto wani jigo wajen hadin kan kasa baki daya. "Mun yi nufin shirya gagarumin taro sai dai Kwankwaso mutum ne mai saukin kan da baya son babban biki."

Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso
Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ladipo Johnson, wata shahararriyar Lauya ta jihar Legas, wadda ta kasance cikin wadanda suka halarci taron ta bayyana cewa, manufar wannan taro shine don haduwar 'yan Najeriya wuri guda domin taya wannan jarumin da ya zamto abin soyuwa a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Illoli 12 na amfani da abincin gwan-gwani

Manyan baki da suka halarci wannan taro sun hadar da Cif Bolaji Ayorinde, Sanata Omoworare, Honorabul Yusuf Danbatta, Alhaji Idi Farouk, Sanata Gbenja Ashafa, Honorabul Garba Michael, Honorabul Bode Mustapha, Injiniya Abubakar.

Sauran manyan bakin sun hadar dar; Alhaji Tajudeen Oyeleye, Dakta Ajibola Raheem, Misis Tokunbo Edun, Mista Wale Ajao, Injiniya Owolabi Solana, Barrista Demola Animashaun da kuma Dakta Ajibola Raheem.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng