Osinbajo ya na sa ran doke Tinubu, Amaechi da kowa a APC, ya zama ‘dan takara a 2023

Osinbajo ya na sa ran doke Tinubu, Amaechi da kowa a APC, ya zama ‘dan takara a 2023

  • Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo yana sa ran ya lashe zaben fitar da gwani a APC
  • Mai ba Shugaban kasa shawara, Sanata Babafemi Ojudu ya ce Osinbajo ya kama hanyar nasara
  • Ojudu ya bayyana cewa alamu sun nuna mataimakin shugaban kasar ne zai rikewa APC tuta a 2023

Abuja - Mai girma mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yana tsammanin zai yi nasara a zaben fitar da 'dan takaran da za a shirya a jam’iyyar APC.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu ya bayyana haka. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto ne a ranar Alhamis.

Sanata Babafemi Ojudu ya shaidawa manema labarai wannan bayan Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen birnin tarayya.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Kawo yanzu mataimakin shugaban Najeriyan ya zauna da ‘yan jam’iyyar APC na jihohi 13 da ke kasar nan da nufin samun kuri’a a zaben fitar da gwani.

Kamar yadda mai ba shugaban kasar shawara ya bayyana, martanin da suke samu daga wajen wadanda aka gana da su ya na kara masu kwarin gwiwa.

Rahoton ya ce Sanata Ojudu ya fadawa Duniya cewa ba a banza su ke zama da ‘yan APC a jihohi ba.

Osinbajo
Yemi Osinbajo a garin Bauchi Hoto: @professoryemiosinbajo
Asali: Facebook

Tsohon Sanatan yana ganin mataimakin shugaban kasar ne zai samu tuta. Hakan ya na nufin zai doke irinsu Asiwaju Bola Tinubu da wasu masu harin tikitin.

Banza ba ta kai zomo kasuwa - Ojudu

“Ba haka nan kurum mu ka zabi mu zagaya duka jihohin nan ba. Ba a banza mu ka nemi mu ji ra’ayin dukkanin masu zaben ‘dan takara ba.”

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

“Ba a banza mataimakin shugaban kasa yake so ya gaisa kuma ya dauki hoto da duk wani mai kada kuri’ar fito da ‘dan takarar da ya gani ba.”
“Za mu iya lissafi daga lokaci zuwa lokaci, yayin da mu ke tafiya. A kimiyyance, mu na duba yiwuwar samun nasara, kuma da alamun dacewa.”
“A duk ranar Duniya, mu ne a kan gaba. A karshe dai, mu ne za mu karbi tutar jam’iyya, dukkaninmu mu na murmushi.” – Babefemi Ojudu.

Kudin kamfe APC ke nema - PDP

Ku na da labari cewa sama da mutum 20 suke neman samun tikitin shugaban kasa a APC. Daga cikinsu har da wasu manyan Ministoci da ke gwamnati.

Hakan ta sa aka ji PDP ta na cewa ana sayen fam din neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ne saboda a tara makudan kudin da za a shiga zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel