Tsohon Hadimin Gwamna Ya Shiga Taƙaddama da Inuwa bayan Shiga Layin Pantami
- Tsohon hadimin Gwamna Muhammadu Yahaya na Gombe ya zargi gwamnan da ƙoƙarin kwace filin al’ummar Kundulum a jihar
- Ya yi zargin cewa gwamnatin Gombe na son amfani da ikonta wajen ƙwace filin al’ummar Kundulum domin mayar da shi harabar Jami’ar Jewel
- Tsohon hadimin ya kuma zargi gwamnan da sa baki a lamarin ’yan sanda da ya shafe shi, yana mai cewa an yi ƙoƙarin tsare shi sau biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Tsohon hadimin Gwamnan Jihar Gombe, Ahmed Shuaibu Gara, ya zargi tsohon mai gidansa da zalunci a jihar.
Gara na zargin Gwamna Inuwa Yahaya da ayyana yaki kansa saboda adawarsa da shirin ƙwace wani fili mallakar al’ummar Kundulum da ke Ƙaramar Hukumar Akko.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani rubutu da dan siyasar ya yi a shafinsa na Facebook wanda ya jawo maganganu daga masu sharhi.
Zargin Gara Gombe ga Gwamna Inuwa
A cewar Gara, ana zargin Yahaya yana da sha’awar mallakar filin Kundulum, don haka ya nemi amfani da ikon gwamnati wajen karɓe shi domin wata ƙungiya mai zaman kanta da ke gudanar da Jami’ar Jewel.
Gara ya kuma zargi gwamnan da sa baki a wani al’amari da ya shafi ’yan sanda da zargin cin zarafi ta yanar gizo, yana tambayar dalilin da zai sa gwamnatin jihar ta tsoma baki a rikicin da ya bayyana a matsayin al’amari na kansa.
Gara, wanda ya yi aiki a matsayin mai ba Yahaya shawara kan harkokin sarrafa bayanai a shekarar 2022, ya ce tun farko yana goyon bayan gwamnan da gwamnatinsa.
Sai dai ya yi zargin cewa dangantakarsa da gwamnatin jihar ta lalace ne bayan ya nuna adawa da abin da ya kira yunƙurin ƙwace filin Kundulum “da ƙarfi” domin bai wa wata jami’a mai zaman kanta.

Kara karanta wannan
Kwamishinan 'yan sandan Kano ya yaba wa Sarki Aminu Ado kan muhimmin abin da ya yi
Gara ya bayyana yadda ya ce ya fuskanci matsala da Gwamna Yahaya, inda ya ce:
“Mai girma gwamna, na girmama ka sosai, na goyi bayanka da gwamnatinka, na yi wa gwamnatinka aiki, amma na lura cewa arangamar kai tsaye ta fara ne bayan matsayin da na ɗauka kan filin al’ummar Kundulum, wanda gwamnatinka ke son ƙwacewa da ƙarfi, wai don amfanin jama’a, sannan ta bai wa wata jami’a mai zaman kanta. Na dakatar da hakan."
Ya yi zargin cewa da farko ana tunkararsa ta hanyar maganganu da wasu mutane da ake amfani da su a madadin gwamnan, kafin lamarin ya rikide zuwa arangama kai tsaye.
A cewarsa, an taɓa ƙoƙarin jefa shi a kurkuku ta hannun ’yan sanda da kotunan majistare, amma yunƙurin bai yi nasara ba.
Tsohon hadimin ya ci gaba da cewa:
“Bari in gaya maka, ranka ya daɗe, ba na tsoron kurkuku. Na taɓa zama a ciki saboda faɗin gaskiya. An yi ƙoƙarin tura ni kurkuku sau biyu, amma abin ya faskara. Amfani da kotunan majistare da ’yan sanda, in sha Allah, ba zai yi nasara a kaina ba. Ya faskara sau biyu."
Gara ya kuma yi zargin cewa wani ɗan kasuwa, Tanko Isyaku Gwamna, wanda ɗan’uwan ɗan takarar gwamnan APC ne a jihar, ya kai shi ƙara kotu da ’yan sanda, lamarin da ya kai ga kama shi a ranar Juma’a.
Gara Gombe ya koma layin Pantami
Kun ji cewa Ahmed Shuaibu Gara Gombe ya nemi afuwar Farfesa Isa Ali Pantami kan kalaman da ya taɓa yi masa a baya.
Gara Gombe ya ce bayan nazarin siyasar jihar Gombe da kuma tarihin aikin Pantami, ya gamsu cewa tsohon ministan zai iya jagorantar jihar zuwa ga ci gaba.
Ya bayyana cewa a wannan karon zai yi aiki tare da shi, duk da cewa ba ya cikin kowace jam'iyyar siyasa, yana mai cewa zai goyi bayan shirin Pantami na 2027.
Asali: Legit.ng

