2023: Uzodinma bai isa ya hana ni takarar shugaban kasa ba - Okorocha

2023: Uzodinma bai isa ya hana ni takarar shugaban kasa ba - Okorocha

  • Dan majalisar tarayya, Sanata Rochas Okorocha, ya yi zargin cewa gwamnan Imo, Hope Uzodinma na yi masa makarkashiya don hana shi takarar kujerar shugaban kasa a 2023
  • Sai dai Okorocha ya ce duk wannan makirci nashi ba zai hana shi yin takarar kujerar Buhari ba
  • Tsohon gwamnan na Imo ya kuma jadadda cewar har gobe shi dan jam'iyyar APC mai mulki ne

Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo kuma dan majalisar tarayya mai ci, Sanata Rochas Okorocha, ya yi zargin cewa Gwamna Hope Uzodinma na kulla-kulla don hana shi takarar kujerar shugaban kasa a 2023.

Da yake zantawa da manema labarai a katafaren gidansa da ke Spilbat, Okorocha mai wakiltan yankin Imo ta yamma a majalisar dattawa, Okorocha ya ce gwamnatin Uzodimma cike take da 'yaudara da karya.'

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya canza magana maimakon fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a jiharsa

2023: Uzodinma bai isa ya hana ni takarar shugaban kasa ba - Okorocha
2023: Uzodinma bai isa ya hana ni takarar shugaban kasa ba - Okorocha Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce daga cikin yaudararsa shine rashin cika alkawarin da ya dauka na ambatan sunayen masu daukar nauyin rashin tsaro a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Ya yi zargin cewa Uzodimma na da wata runduna mai suna ‘Hopism Strike Force’.

Hakazalika, Okorocha ya yi watsi da zarge-zargen da Uzodimma yayi masa na cewa yana tube masa ikon da yake da shi a matsayin gwamna.

Okorocha ya ce:

"Na yi gwamna tsawon shekaru takwas kuma a yanzu ina rike da mukamin sanata. Ba zan sake takarar gwamna ba haka kuma ba zan yi takarar majalisar dattawa ko wakilai ba. Zan je matakin tarayya ne kawai. Matsalana da shi kawai na iya zama saboda ina son yin takarar shugaban kasa ne, wanda yake kokarin dakatar da ni ko kuma surukina wanda ka iya takara da shi a 2023. Amma bari na fada maku, Uzodimma ba zai iya hana ni takarar shugaban kasa kuma idan yana so ya gwada yin hakan, ina jiransa."

Kara karanta wannan

Daga karshe: 'Yan kasa sun tafka zanga-zanga, firaministan Sudan yayi murabus

Rahoton ya kuma kawo cewa Okorocha ya musanta zargin cewa yana son ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Ya ce a matsayinsa na dan jam’iyyar APC, har yanzu yana cikin jam’iyya mai mulki.

Gwamna ya fasa fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a jiharsa

A baya mun kawo cewa Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya gaza bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin rashin tsaro kamar yadda ya yi alkawarin yi yau Talata 4 ga watan Janairu.

Jaridar Vangaurd ta bibiyi jawabin gwamnan a wurin taron masu ruwa da tsaki na jihar Imo, wanda ya gudana a gidan gwamnatin jiha.

Amma Uzodinma ya yi kira ga sanata mai wakiltar jihar Imo ta yamma Rochas Okorocha, ya kyale shi haka nan ya jagoranci jihar Imo cikin kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng