Tsohon Shugaban Najeriya Shehu Shagari ya isa shekara 93
Shehu Usman Aliyu Shagari wanda ya mulki Najeriya daga 1979 zuwa 1983 ya cika shekaru 93 a Duniya a jiyan nan. Don haka ne mu ka kawo maku kadan daga cikin tarihin tsohon Shugaban kasar da Shugaba Buhari ya kifar a 1983.
An haifi Turakin Sokoto Alhaji Shehu Shagari a Ranar 25 ga Watan Fubrairun 1925 ya kuma rike matsayin Minista sau kusan 7 a kasar daga bayan yakin basasa a 1958 zuwa 1975. Kafin nan Shagari yayi aiki a matsayin Malamin Makaranta.
Shagari ya fara siyasa ne tun a 1951 lokacin da ya zama Sakataren Jam'iyyar NPC ta Arewa a Sokoto. A 1954, Shagari ya zama ‘Dan Majalisa na Yammacin Jihar Sokoto. Bayan nan kuma ya zama Sakataren Firayim Minista na lokacin Abubakar Tafawa Balewa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Malaman Makaranta
Shehu Shagari ya rike Ministan kasuwanci bayan nan kuma ya zama Ministan tattali a 1960. Daga nan ne aka nada Shagari Ministan fansho. A 1962 aka maida Shagari Ministan cikin gida gar zuwa lokacin juyin mulki. Bayan nan ya rike wasu mukaman kuma.
An cigaba da damawa da Shagari a Gwamnati har bayan Gwamnatin Shugaba Gowon. Shagari ya rike mukamai a ma’aikatar kudi da bankin Duniya da Hukumar lamuni ta Duniya IMF. A 1978 aka kafa Jam’iyyar NPN inda yayi takara ya kuma zama Shugaban kasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng