Tazarce: An Zakulo Manyan Abubuwa 6 da Za Su Taimaka wa Tinubu Ya Ci Zabe a 2027
- Jam’iyyar APC ta sake tabbatar da Bola Tinubu a matsayin dan takararta a zaben 2027, domin ya jagoranci kasar har zuwa 2031
- Sai dai, APC da kuma ita kanta gwamnatin Tinubu na fuskantar kalubale na matsin tattali, tabarbarewar tsaro da rashin ayyukan yi
- Duk da wadannan matsaloli, Legit Hausa ta zakulo wasu manyan abubuwa shida da za su iya taimakawa Tinubu ya lashe zaben 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Yayin da Najeriya ta yi bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, jam'iyyu da 'yan siyasa sun kara daura daramar tunkarar zaben 2027.
Shugaba Bola Tinubu, wanda ya lashe zaben 2023 da 36.6% na kuri’un da aka kada a karkashin APC, ya samu goyon bayan jam’iyyarsa a hukumance domin neman tazarce.

Source: Twitter
Alamomin nasarar Bola Tinubu a 2027
Wannan goyon bayan da aka sanar a watan Mayu 2025 na nuna irin kwarin gwiwar APC ga shugabancin Tinubu, duk da sukar da gwanmnatinsa ke sha kan matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro, inji rahoton Reuters.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan kusoshin Najeriya kamar mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, sun ce Tinubu ya cancanci yin tazarce saboda sauye-sauyen da yake yi.
A wannan rahoton, mun duba manyan abubuwa shida da za su iya taimaka wa Shugaba Bola Tinubu ya lashe zaben 2027 cikin sauki.
1. Sauya shekar gwamnoni zuwa APC
Daga watan Yuni 2025, APC na rike da jihohi 23 cikin 36, bayan samun karin gwamnoni uku daga PDP da suka koma jam’iyyar: Sheriff Oborevwori na Delta a Afrilu, Umo Eno na Akwa Ibom a Yuni, da Peter Mbah na Enugu a Satumba.
A ranar 1 ga Oktoba, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya nuna cewa wasu gwamnoni ma na shirin komawa APC, yana danganta hakan da nasarorin gwamnatin Tinubu.
Masana dai sun yi gargadi cewa wannan yawaitar sauya sheƙar na rushe siyasa mai akida, yana mayar da jam’iyyu gidajen mutum daya, cewar rahoton Business Day.
2. Raunin jam’iyyun adawa
Vanguard ta rahoto cewa PDP ta rasa iko a jihohi da dama, yanzu tana rike ne da jihohi goma kawai; Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Enugu, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Taraba da Zamfara.
Jam’iyyar LP kuwa ta fuskanci rikice-rikice bayan hukuncin kotu kan shugabancinta, sannan an ga sama da dubunnan mambobin adawa na sauya sheka zuwa APC tsakanin 2024 da 2025 saboda sabani.
Masana na ganin cewa kuri’un PDP da LP da suka kai miliyan 13 a 2023 ba za su iya zama barazana ga APC a 2027 ba idan ba su hade ba.
Ana ganin, rashin hadewar jam'iyyun adawa ne ya ya bai wa APC damar lashe zabe a jihohin Bayelsa, Edo, Kogi da Ondo.
3. Burin yin takarar Atiku da Obi
Atiku Abubakar mai shekaru 78 ya jagoranci kaddamar da jam’iyyar hadakata ta ADC a watan Yuli 2025, inda ya kuma bayyana burinsa na tsayawa takara karo na kusan bakwai.
Shi ma dai Peter Obi, mai shekaru 63, a watan Yunin 2025, ya bayyana cewa zai tsaya takara, kuma zai yi wa’adi daya ne kacal, sannan ba zai amince da yi wa Atiku mataimaki ba.
Irin wannan ta faru a zaben 2023, na rashin hadakar 'yan adawa, inda Atiku ya samu 29% na kuri'un da aka kada, Obi ya tashi da 25%, lamarin da ya ba Tinubu nasara.
4. Rashin hadin gwiwar siyasa
Hadakar 'yan adawa karkashin ADC da aka kulla a watan Yulin 2025 ta hada da Atiku, Obi, David Mark, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, Rauf Aregbesola da dai sauransu.
Amma rikicin shugabanci ya fara rusa wannan hadaka, inda aka ga PDP ta ki shiga, yayin da jam'iyyar LP ta nesanta kanta daga hadakar.
Masu sharhi sun ce wannan hadin gwiwa ba shi da karfi kamar na 2013 da ya kafa APC, saboda ya dogara da son ran 'yan hadakar ba da akida ba.
Duk da haka, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, Atiku ya sanar da cewa akwai kusoshin APC, PDP, LP da ke cikin hadakar ADC, da za ta kayar da Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan
"Mun ceto Naira," Tinubu ya tabo batun darajar kudin Najeriya a jawabin ranar 'yanci

Source: Twitter
5. Tsarin karba karba na mulkin Najeriya
Saboda tsarin rabon mulki na bai wa Kudu dama a 2027 bayan mulkin Arewa na shekaru takwas a hannun Buhari, tuni PDP ta tura tikitin ta zuwa Kudu a watan Agusta 2025.
Kai tikitin da PDP ta yi zuwa Kudu, ya sa wasu kungiyoyi sun fito sun nuna cewa an nuna wariya ga Arewa, kuma hakan zai iya sa Tinubu ya amfana da wannan rashin hadin kan.
Jaridar Punch ta rahoto cewa yanzu haka an samu baraka a Arewa, inda shugaban kungiyar AYCF, Yerima Shettima ya ce matakin PDP ya take doka, ya nuna wariya ga Arewa da 'yancin takara.
6. Lissafin ‘yan siyasar Arewa
Manyan jiga-jigan Arewa sun fi mayar da hankali ga samun damar shugabanci mai dorewa fiye da takarar Atiku a 2027, saboda suna ganin nasararsa za ta toshe nasarar Arewa a 2031.
Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, ya roƙi 'yan Arewa da su "jira har sai 2031" bayan mulkin Tinubu sannan su karbi mulki, inji Bayo Onanuga a shafinsa na Facebook.
Anthony Sani na ƙungiyar ACF ya yi hasashen Tinubu zai ci zaɓe a 2027 saboda tasirin Buhari da kuma batun karba karbar mulki da ake yi a tsakanin shiyyoyin kasar.
Atiku ya mayar da martani kan hakan, yana cewa akwai rashin daidaiton shugabanci tsakanin Arewa da Kudu, inda ya ce Arewa ta yi shekara 11 ne kan mulki yayin da Kudu ta yi 17.
Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan tazarcen Tinubu
Wasu 'yan Arewa da muka zanta da Legit Hausa ta zanta da su game da tazarcen Tinubu sun yi tsokaci daban daban.
Nura Haruna Maikarfe daga Katsina ta ce:
"A zahirin gaskiya yana kokari, ka san kowanne shugaban kasa da bangaren da ya fi mayar da hankali a kansa. Ni na fi ganin kamar ya fi karkata kan tattalin arziki.
"Idan kuma ka lura, tun daga hawansa mulki zuwa yanzu, tsare-tsarensa sun fi ta'allaka kan tattali, haraji, da sauran hanyoyin samun kudin shiga. To a wannan fuskar yana kokarin kawo sauyi, wanda hakan ne ma ya jawo tsadar rayuwa a kasar.
"To mu ba wannan ne matsalar mu ba a yanzu. Mu nan shiyyar Arewa maso Yamma ba abin da muke so sama da zaman lafiya, amma yau ina zaman lafiyar yake? Babu.
"Kullum ana kashe mu, ana garkuwa da mu, ana tilasta mu biyan kudin fansa, an hana mu noma ko kasuwanci, kowa ya koma yin rayuwa cikin dari-dari."
Nura Haruna ya ce yayin da ake ganin ci gaba a wasu shirye-shiryen Tinubu, akwai bukatar gwamnati ta mayar da hankali kan tsaro a Arewa.
Ashiru Aliyu Tafoki ya ce:
"Ni da ka ganni nan, ban taba samun alheri mai yawa irin a mulkin Tinubu ba. A mulkin Tinubu na yi aure, na mallaki fili har na fara gini, ga shi jiya-jiyan nan na sayi babur.
"To ka san an ce mutuwar wani tashin wani. Nasarorin da na samu ba yana nufin Tinubu ne ya ba ni ba, kawai dai na samu a mulkinsa ne, wanda kowa ke kuka da shi.
"Mu dai sai hamdala, muna kuma rokon Allah ya sassauta mana, ya kawo mana zaman lafiya da kuma karin yalwar arziki."
Amina Lawal daga Kaduna ta ce:
"Muna jin dadin mulki Tinubu, ba ma jin dadi. Shi ta wasu fuskokin yana kokari, ta wasu bangarorin kuma ya gaza sosai wallahi.
"Ba zan wani yi dogon sharhi ba, kawai dai a gyara idan za a gyara, mutane su samu saukin rayuwa, abinci ya wadata, idan kuma aka ki, to 2027 na nan zuwa ai."
Abubuwa 2 za su hana Tinubu tazarce
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sanata Ali Modu Sheriff ya ce abubuwa biyu ne kacal za su iya hana Shugaba Bola Tinubu zarcewa a zaben 2027.
Modu Sheriff ya yi ikirarin cewa rashin yin zabe gaba daya ko kuma janyewar Tinubu daga zabensa da kansa ne kawai za su iya hana shi tazarce.
Tsohon gwamnan ya buga kirji da cewa, da irin tsarin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, nasararsa a zaben 2027 za ta zama kamar kiftawar ido ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng





