Dalilan Jam'iyyar NNPP na Raba Gari da Sanata da Ƴan Majalisa 5 a Jihar Kano

Dalilan Jam'iyyar NNPP na Raba Gari da Sanata da Ƴan Majalisa 5 a Jihar Kano

Rikicin cikin gida a jam’iyyar NNPP, musamman a ɓangaren Kwankwasiyya a Kano ya jawo an kori wasu daga cikin manya a tafiyar siyasar.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Daga hawan NNPP mulki a Kano a shekarar 2023, an samu ɓaraka da rashin fahimta a tsakanin manya, da ma ƙananan ƴan jam'iyya, wanda aka rika dakatar da su, kafin wasu su bar Kwankwasiyya

Daga cikin manyan ƴan majalisa ya shafa akwai Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum.

NNPP ta yi kora
Sanata Kawu Sumaila da Hon. Kofa da Hashimu Dungurawa Hoto: Saifullah Sale/AbdulMumin Jibrin/Tasi'u Y Ladan
Source: Facebook

Sauran su ne Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, Hon. Abdullahi Sani Rogo, da kuma Hon. Aliyu Sani Madakin Gini.

Rikicin da ya jawo su ka fice daga NNPP, bayan jam'iyya a karkashin Hashimu Dungurawa ya dakatar da su ya samo asali ne daga zargin yi wa jam'iyya zagon kasa, kamar yadda za a karanta a wannan rahoto:

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama wiwi mai nauyin kilo 112 a wajen hadarin mota a Kano

1. NNPP ta dakatar Sanata Kawu Sumaila

Jaridar Leadership ta wallafa cewa a farkon shekarar 2025, NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila daga jam’iyyar a Kano, inda aka ce akwai alamun rashin biyayya ga jam'iyya da kuma hada kai da ƴan adawa. Bayan rikicin ya ƙara kamari, Sumaila ya sanar da barin NNPP gaba ɗaya, kuma daga bisani ya sanar da cewa ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Sanata Masu Sumaila ya bar NNPP
Hoton Hon. Kawai Sumaila da Hashimu Dungurawa Hoto: Senator AbdulRahman Kawu Sumaila/Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

A cewar sa, ya dauki matakin ne bayan ya yi shawara da ƴan mazaɓarsa da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce:

“Na ɗauki wannan mataki ne domin ci gaban jama’ar da nake wakilta."

2. Rurum ya bar NNPP/Kwankwasiyya bayan dakatar da shi

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Hon. Kabiru Alhassan Rurum, tsohon kakakin majalisar dokokin Kano kuma ɗan majalisa mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure, shi ma ya shiga jerin wadanda aka dakatar a watan Fabrairu 2025.

Shugabancin NNPP a Kano ya bayyana shi a matsayin wanda yake cin amanar jam'iyya amma Rurum ya yi watsi da wannan hukunci.

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

An kori Alhassan Rurum daga NNPP
Hoton Hon. Alhassan Rurum Hoto: Fatihu Yusuf Abdullahi
Source: Facebook

A wata hira ya yi, ya bayyana cewa dakatarwar ba ta da tushe balle makama, yana mai cewa shi yana wani tsagin NNPP na daban na ɓangaren Kwankwasiyya ba.

3. Hon. Abdullahi Sani Rogo

Abdullahi Sani Rogo, wani fitaccen ɗan majalisa daga Kano, ya shiga jerin wadanda aka dakatar daga NNPP a rikicin Fabrairu 2025.

Shugabannin jam’iyyar a jihar sun ce wannan dakatarwa na da alaƙa da zargin rashin biyayya da kuma yin ayyukan da suka saba wa NNPP.

Shugaban NNPP a Kano, Dr. Hashimu Dungurawa ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da aikata ayyukan da ke cutar da jam’iyyar zai fuskanci hukunci

4. Hon. Aliyu Sani Madakin Gini

Aliyu Sani Madakin Gini, wakilin mazabar Dala, shi kuwa ya sanar da barin Kwankwasiyya, inda ya ce akwai matsala a karkashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso.

Madakin Gini ya ce salon jagoranci da rashin daidaiton ra’ayi ya tilasta masa wannan mataki.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Rigima ta barke a jam'iyyar Kwankwaso bayan korar da dan Majalisa a Kano

Madakin Gini ya watsar da Kwankwasiyya
Hoton Aliyu Madakin Gini da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Aliyu Sani Madaki, Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya bayyana cewa yana nan daram a jam'iyyar NNPP, duk da cewa ya ce yana tsagin Mas'ud Doguwa, amma ya raba gari da Kwankwasiyya.

5. An kori Hon. Abdulmumin Jibrin

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, shi ne na baya-bayan nan da NNPP ta kora a Kano, kuma lamari ya dauki hankali sosai.

Shugabancin NNPP ya sanar da korarsa daga jam’iyyar bisa zargin rashin biyayya ga jam'iyya da kin biyan kudin jam'iyya.

Sannan NNPP ta ce ta fusata bayan da Kofa ya yi barazanar zai fice daga cikin jam'iyyar, kuma yana da damar hakan.

Hon Kofa ya bar NNPP
Hon Jibrin Kofa Hoto: AbdulMumin Jibrin Kofa PhD
Source: Facebook

Bayan an sanar da korarsa, Hon. Kofa ya bayyana mamaki a kan matakin, yana mai cewa an yi masa rashin adalci.

Shi ma daga baya ya sanar da cewa ya fice daga NNPP, kuma har lokacin haɗa wannan rahoto, bai sanar da inda ya koma ba.

NNPP ta kare matakin korar ƴaƴanta

Shugaban NNPP na Kano, Dr. Hashimu Dungurawa ya shaida wa Legit cewa matakin dakatarwa da korarwasu daga cikin manyan ƴaƴanta na da nasaba da kare mutuncin sauran yan jam'iyya.

Kara karanta wannan

Bayan katoɓararsa, NNPP ta kori Jibrin Kofa daga jam'iyyar, ta jero wasu dalilai

Hashimu Dungurawa ya ce:

"Duk wanda mu ka kora dinnan, kamata ya yi masu son ci gaban wannan jam'iyya su gode mana, su kuma tafa mana, su ce wannan abu da muka yi, Allah Ya saka mana da alheri kuma lallai mun yi jihadi."
"Ba karamin abu ba ne mutum yana da arziki a hannunsa, amma ka ce ka hakura ya tafi harkarsa, kai ka san wuyan da ka hango, ba ta wasa ba ce."
"Mutane ne masu ƙaramin tunani."

Ya kara da cewa wasu daga cikin yan jam'iyya da aka kora kamar cutar daji ne ga NNPP, kuma dole a ɗauki matakin yanke su daga jam'iyya kafin su 'lalata' wasu.

A kalamansa:

"Ida hannunka daya ya kamu da cutar daji, sai a ce a yanke shi a zubar, ai da takaici a ce ka yanke hannunka ka zubar ba, amma idan ba ka yanke ba, ai ka ga za a yi asarar gaba daya jikin."

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

"To wadannan mutanen, sunansu ke nan a jam'iyyance."

Tsagin NNPP ya nemi sulhu da Kwankwaso

A baya, mun wallafa cewa tsagin NNPP, reshen jihar Kano, ya bayyana damuwarsa bayan sauya sheƙar wasu daga cikin jiga-jiganta ke koma wa APC.

Mas’ud El-Jibril Doguwa, shugaban tsagin NNPP a Kano, ya ce lokaci ya yi da za a yi taron gaggawa domin lalubo mafita ga rikicin da ke ci gaba da yi masu barazana.

Doguwa ya bayyana cewa sauya sheƙa ba sabon abu ba ne a siyasa, amma ya zargi Kwankwasiyya da samun mummunan saɓani da sauran yan jam'iyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng