Ganduje: Jerin Shugabannin APC da yadda Suka Sauka daga Shugabanci

Ganduje: Jerin Shugabannin APC da yadda Suka Sauka daga Shugabanci

Shugabanni takwas ne suka jagoranci jam'iyyar APC daga kafa ta a 2013 zuwa yau, wadanda suka jagoranci jam'iyyar sun sauka daga kujerar saboda dalilai daban daban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Murabus da tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya yi a makon da ya wuce ya sanya jama'a waiwaye kan shugabannin jam'iyyar da suka gabata.

Galibi shugabannin jam'iyya a Najeriya suna sauka ne bayan an samu sabani ko rashin jituwa wajen jagorantar majalisar NWC.

Wasu daga cikin wadanda suka jagoranci APC a baya
Wasu daga cikin wadanda suka jagoranci APC a baya. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin mutanen da suka shugabanci APC da yadda suka sauka daga kujerar shugabancin jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Bisi Akande: Shugaban rikon APC na farko

An nada Cif Bisi Akande a matsayin shugaban rikon kwarya na farko a watan Fabrairu 2013, bayan haɗuwar manyan jam’iyyun ACN, CPC, ANPP da wasu daga PDP.

Kara karanta wannan

Bayan Ganduje, APC ta budewa Kwankwaso kofar sauya sheka da aiki da Bola Tinubu

Ya shugabanci jam’iyyar na tsawon kusan shekara guda kafin zaɓen shugaban dindindin a babban taron APC da aka yi a watan Yuni 2014.

Bisi Akande da ya fara rike shugabancin APC
Bisi Akande da ya fara rike shugabancin APC. Hoto: All Progessive Congress
Source: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Osun ne daga 1999 zuwa 2003, kuma ya kasance cikin gwanayen da suka kafa sabuwar jam’iyyar APC.

Bisi Akande ya sauka bayan kammala aikinsa na riko tare da gina tushe mai ƙarfi ga sabuwar jam’iyyar.

2. John Oyegun: Shugaban dindindin na farko

Tsohon gwamnan Edo daga 1992 zuwa 1993, John Oyegun ya zama shugaban farko na dindindin na jam’iyyar APC a watan Yuni 2014 kamar yadda PM News ta rahoto.

Ya jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu har zuwa Yuni 2018, lokacin da wa’adinsa ya ƙare, kuma ya mika ragamar mulki a babban taron jam’iyyar.

Tsohon zababben shugaban APC na farko, John Oyegun
Tsohon zababben shugaban APC na farko, John Oyegun. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

A karkashinsa, jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zaɓen 2015, inda Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa.

3. Adams Oshiomhole: Shugaban APC da kotu ta dakatar

Adams Oshiomhole ya karɓi shugabancin APC a ranar 23 ga Yuni 2018 bayan saukar John Oyegun.

Tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ne da kuma tsohon gwamnan Edo daga 2008 zuwa 2016.

Kara karanta wannan

Saukar Ganduje daga shugabancin APC ya bar babban giɓi a APC, an sa ranar taron NEC

Tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole
Tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole. Hoto: All Prgressive Congress
Source: UGC

Sai dai jagorancinsa ya kasance cike da rikice-rikice na cikin gida. A watan Nuwamba 2019, shugabannin kananan hukumomi 18 a jihar Edo sun bayyana rashin yarda da shi.

A ranar 16 ga Yuni 2020, kotun daukaka ƙara ta tabbatar da dakatar da shi daga kujerar shugabanci.

4. Mai Mala Buni: Shugaban riko na kwamitin wucin-gadi

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karɓi shugabancin jam’iyyar APC a ranar 25 ga Yuni, 2020 bayan rushewar kwamitin gudanarwa na Adams Oshiomhole da hukuncin kotu.

An naɗa shi a matsayin shugaban rikon kwarya na kwamitin CECPC da nufin sasanta rikice-rikicen cikin gida da kuma shirya babban taron jam’iyya.

Gwamnan Yobe da ya jagoranci APC a baya
Gwamnan Yobe da ya jagoranci APC a baya. Hoto: Yobe State Government
Source: Twitter

Tun da farko, an ba shi wa’adin watanni shida, amma an ci gaba da tsawaita wa’adin har zuwa Maris 2022, inda ya jagoranci shirya babban taron APC na kasa.

A wannan taro ne aka zabi sabon shugaban jam’iyya, sanata Abdullahi Adamu, wanda hakan ya kawo ƙarshen shugabancin riko na Buni bayan kusan shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Abba Kabir da gwamnonin adawa 4 da jam'iyyar APC ke son jowowa kafin 2027

5. Abdullahi Adamu ya sauka dalilin murabus

Business Day ta rahoto cewa Abdullahi Adamu ya zama shugaban APC a Maris, 2022 ta hanyar da aka cimma sulhu tsakanin fannonin jam’iyyar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Adamu ya shugabanci jam’iyyar a lokacin zaben 2023 da ya haifar da nasarar Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Abdullahi Adamu a lokacin da yake shugabancin APC
Abdullahi Adamu a lokacin da yake shugabancin APC. Hoto: All Progressive Congress
Source: UGC

Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa kafin karewar wa’adinsa, rahotanni sun ce matsin lamba daga cikin gida da rashin jituwa da sababbin shugabanni ne ya tilasta masa sauka.

6. Abubakar Kyari: Shugaban riko kafin Ganduje

Bayan saukar Abdullahi Adamu, mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (Arewacin Najeriya), Sanata Abubakar Kyari, ya karɓi shugabancin APC a matsayin shugaban riko.

Rahotan Channels TV ya nuna nuna cewa Sanata Abubakar Kyari ya jagoranci jam’iyyar daga 17 ga Yuli zuwa 3 ga Agusta, 2023.

Sanata Kyari da ya shugabanci APC kafin Ganduje
Sanata Kyari da ya shugabanci APC kafin Ganduje. Hoto: Senator Abubakar Kyari
Source: Twitter

Daga karshe, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya karɓi ragamar shugabanci a ranar 3 ga Agusta, 2023.

7. Ganduje ya sauka ta hanyar murabus

Kara karanta wannan

'Ganduje ya jawo wa Kano abin kunya,' NNPP ta yi magana kan komawar Kwankwaso APC

An naɗa Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC a ranar 3 ga Agusta, 2023, bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu daga kujerar.

Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje a ofis
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje a ofis. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

Ganduje ya hau mulki a wani lokaci da jam’iyyar ke buƙatar daidaito da ƙarfin shugabanci domin tabbatar da cigaba bayan zaben shugaban kasa da Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara.

Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus saboda dalilan rashin lafiya duk da cewa wasu rahotanni sun nuna cewa tilasta shi aka yi.

8. Dalori ya karɓi rikon APC bayan Ganduje

Biyo bayan saukar Ganduje, Hon. Ali Bukar Dalori, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa daga Arewa, ya karɓi ragamar shugabanci a matsayin shugaban rikon kwarya.

Ganduje na muka mulkin APC ga Dalori
Ganduje na muka mulkin APC ga Dalori. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Wannan dai na zuwa ne kafin gudanar da wani babban taro na kwamitin jam’iyya da zai tantance wanda zai zama sabon shugaban jam’iyyar na dindindin.

APC ta tabbatar da murabus din Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta tabbatar da murabus din tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.

Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus ne sakamakon rashin lafiya kamar yadda APC ta tabbatar da hakan.

APC ta yaba wa Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarin da ya yi a lokacinsa, tare da yi masa fatan alheri a abubuwan da ya saka a gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng