2013 Zuwa 2023: Jerin Sunayen Wadanda Suka Shugabanci Jam'iyyar APC Zuwa Yau Da Gudumawarsu

2013 Zuwa 2023: Jerin Sunayen Wadanda Suka Shugabanci Jam'iyyar APC Zuwa Yau Da Gudumawarsu

  • Tarihin jam'iyyar APC ya faro ne tun daga 2013 bayan jam'iyyun adawa uku sun hade a kasar
  • Hadewan bai rasa nasaba da yunkurin kwace mulki daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar a wancan lokaci
  • Bayan shekaru biyu, jam'iyyar ta kwace mulki daga PDP bayan shekaru 16 suna mulki a kasar

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta mamaye harkar siyasar Najeriya tun bayan kirkirar ta a 2013.

An kirkiri jam'iyyar ce daga gamayyar jam'iyyun adawa a wancan lokaci da suke hamayya da jam'iyyar PDP.

Daga 2013 Zuwa 2023: Jerin Sunayen Wadanda Suka Shugabanci Jam'iyyar APC Zuwa Yanzu
An Kirkiri Jam'iyyar APC A Shekarar 2013 Bayan Hadakar Jam'iyyun Adawa A Kasar. Hoto: Abubakar Kyari.
Asali: Facebook

Gamayyar jam'iyyun da suka yi hadaka don gina APC sun hada da ACN da CPC da NNPP.

Jam'iyyar ta samu sauye-sauye na shugabanni kamar sauran jam'iyyu na kasar tun 2013.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Na Hannun Daman Buhari Suka Tsinci Kansu A APC Bayan Zuwan Tinubu

Legit.ng ta tattaro muku jerin sunayen shugabannin jam'iyyar tun daga 2013 zuwa yau da kuma gudumawar su.

1. Cif Bisi Akande (2013-2014)

Tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande ya rike shugabancin jam'iyyar na rikon kwarya na dan lokaci kadan.

Ya yi kokarin hada kan jam'iyyun adawa don ganin an wafce mulki daga jam'iyyar PDP a wancan lokaci.

Har yanzu ana damawa da shi a jam'iyyar kuma yana daga cikin masu ruwa da tsaki.

2. Cif John Oyegun (2014-2018)

John Oyegun shi ya fi kowa dadewa a kan shugabancin jam'iyyar tun bayan kafa ta.

Bayan samun rijista a matsayin jam'iyya, Oyegun shi ne ya fara zama halastaccen shugaban jam'iyyar.

A lokacin shi ne jam'iyyar ta samu nasara a babban zabe da aka gudanar a 2015 da a karon farko jam'iyyar adawa ta kwace mulki a hannun mai ci.

Daga 2013 Zuwa 2023: Jerin Sunayen Wadanda Suka Shugabanci Jam'iyyar APC Zuwa Yanzu Da Gudumawarsu
An Kirkiri Jam'iyyar APC A Shekarar 2013 Bayan Hadakar Jam'iyyun Adawa A Kasar. Hoto: Akande/Adamu/Kyari/Oyegun.
Asali: Facebook

3. Kwamred Adams Oshiomhole (2018-2020)

Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Oshiomhole ya karbi shugabancin jam'iyyar a 2018.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Najeriya Yayin da Rikicin APC Ya Yi Kamari

A lokacinshi, saboda irin mulkin karfi da ya ke, jam'iyyar ta samu nasarori da dama a jihohi daban-daban.

Sai dai a lokaci guda kuma, jam'iyyar ta sha fama da matsalolin cikin gida da yasa aka sauke shi a shugabancin jam'iyyar.

4. Mai Mala Buni (2020-2022)

Gwamnan jihar Yobe mai ci, Mala Buni ya rike shugabancin jam'iyyar na rikon kwarya bayan matsalolin da suka dabaibaye jam'iyyar.

Bayan wargaza kwamitin tsare-tsare na jam'iyyar, Buni ya rike shugabancin jam;iyyar na rikon kwarya kafin daga bisani ya zama shugaban jam'iyyar halastacce.

Yayin mulkin jam'iyyar, Buni ya yi kokarin kawo sauyi da kuma hada kan 'yan jam'iyyar, cewar BBC Pidgin.

5. Sanata Abdullahi Adamu (2022-2023)

Adamu shi ne shugaban jam'iyyar da ya fuskanci matsaloli kafin darewa kujerar bayan dadewa da ya yi a jam'iyyar PDP mai adawa.

A kwanakin nan ya bayyana cewa bai goyi bayan Shugaba Tinubu ba yayin gudanar da zaben fidda gwani a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Riko Na Jam'iyyar APC

A ranar Lahadi 16 ga watan Yuli, Sanata Adamu ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar.

6. Sanata Abubakar Kyari (2023-Zuwa Yanzu)

Bayan murabus na Abdullahi Adamu, Abubakar Kyari wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar a Arewa ya karbi shugabancin jam'iyyar.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa an sanar da Kyari a matsayin shugaban jam'iyyar na rikon kwarya a ranar Litinin 17 ga watan Yuli a Abuja.

Kyari wanda ya wakilci Borno ta Arewa a majalisar Dattawa ta tara shi ya jagoranci zaman masu ruwa da tsaki a ranar Litinin 17 ga watan Yuli.

Shugaban APC, Sanata Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa

A wani labari makamancin wannan, tsohon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya magantu a kan murabus da ya yi na shugabancin jam'iyyar.

Sanata Adamu ya mika takardar murabus din sa ne a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli ga fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gano Hanyar Wargaza LP, Zai Ba Na-Hannun Daman Peter Obi Kujerar Minista

Ya ce zai yi bayani a kan dalilin murabus din nasa daga shugabancin jam'iyar da zarar shugaban kasa, Bola Tinubu ya dawo daga Nairobi ta kasar Kenya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.