Da duminsa: Jam'iyyar APC ta tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan Gwamna Mai Mala Buni

Da duminsa: Jam'iyyar APC ta tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan Gwamna Mai Mala Buni

  • Karo na biyu, an sake tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan APC
  • Gwamna Mai Mala Buni zai cigaba da jan ragamar harkokin jam'iyyar
  • Da farko an shirya yin taron gangamin zaben sabbin shugabanni a watan Yuni

Uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryar dake karkashin jagorancin Gwamna jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni.

Dirakta Janar na yada labaran gwamna Buni, Mamman Mohammed, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a, rahoton DT.

Legit ta kawo muku rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe kuma shugaban kwamitin kula da tsare-tsaren taron jam'iyyar APC (CECPC).

Buhari Sallau, mai taimaka wa shugaban kasa kan kafafen yada labarai ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Juma’a, 25 ga Yuni.

KU KARANTA: Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun

Gwamna Mai Mala Buni da BUhari
Da duminsa: Jam'iyyar APC ta tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan Gwamna Mai Mala Buni Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA NAN: An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

An kafa kwamitin rikon kwaryar ne ranar 25 ga Yuni, 2020, bayan da kotu ta fitittiki Kwamred Adams Oshiomole daga jam'iyyar.

Shugaba Buhari ya kafa kwamitin rikon kwaryar domin kwantar da kura da kuma dinke barakar dake tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.

Bayan watannin shida na farko da aka baiwa kwamitin, an sake tsawaitawa da wata shida.

Wannan shine karo na uku da za'a tsawaita wa'adin kwamitin.

Ga jerin sunayen mambobin kwamitin:

Gwamna Mai Bala Buni (Yobe)

Gwamna Isiaka Oyetola

Ken Nnamani

Stella Okorete

Gwamna Sani Bello (North Central)

Dr. James Lalu

Sen. Abubakar Yusuf

Hon. Akinyemi Olaide

David Lyon

Abba Ari

Prof. Tahir Mamman

Ismail Ahmed

Sen. Akpan Udoedehe

Asali: Legit.ng

Online view pixel