Rikicin Kano: Mala Buni ya yi zama da Shekarau da manyan APC da ke fada da Ganduje

Rikicin Kano: Mala Buni ya yi zama da Shekarau da manyan APC da ke fada da Ganduje

  • Shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni yana ta kokarin dinke barakar da ta ke jihar Kano
  • Gwamna Mai Mala Buni ya yi taro da jiga-jigan jam’iyyar APC na reshen jihar Kano a garin Abuja
  • Ibrahim Shekarau da wasu ‘yan majalisar Kano a karkashin APC sun samu halartar zaman a jiya

Abuja - Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa, Mai Mala Buni ya hadu da ‘yan tawaren APC na jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Mai Mala Buni ya yi zama da jagororin jam’iyyar ta APC mai mulki na reshen jihar Kano a yammacin Talata a Abuja.

Kawo yanzu ba mu samu labarin matsayar da aka cin ma bayan wannan tattaunawa da aka yi ba.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Majiya ta shaidawa jaridar cewa an yi wannan zama ne da nufin kawo karshen sabanin da ake samu tsakanin manyan ‘ya ‘yan APC da bangaren gwamnati.

Darekta Janar na harkokin yada labarai na gwamna Mai Mala Buni watau Mamman Mohammed ya tabbatar da cewa an yi wannan zama a birnin tarayya Abuja.

Taro da Mala Buni
Taron hada kan APC a Kano Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mohammed ya ce manyan ‘yan siyasar sun hadu ne a gidan gwamnatin jihar Yobe da ke Abuja. Shugaban jam’iyyar APC na riko shi ne ya jagoranci zaman.

Wadanda aka yi zaman da su

Rahoton ya bayyana cewa duka Sanatocin jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, Barau Jibrin da Kabiru Gaya sun samu halartar wannan zama da aka yi a jiyan.

Daga cikin sauran wadanda aka gani a taron akwai tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara da kuma Honarabul Alhassan Ado Doguwa.

Kara karanta wannan

2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara

Alhassan Ado Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai na kasa yana tare da bangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba sashen G7 ba.

A zama na karshe da aka yi a makon jiya, tsohon gwamna Shekarau ya tabbatar da cewa za su cigaba da zama da kwamitin Buni domin a shawo kan sabaninsu.

Ahmad Prince Gandujiyya ya fitar da hotunan wannan zama da aka yi a shafinsa na Facebook.

Shari'ar Ganduje da Shekarau

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake sa ran sauraron shari'ar da kotun daukaka kara za tayi a karar gwamnatin Abdullahi Ganduje da bangaren G7 da ke yaki da shi.

A baya an ji cewa wani Alkalin kotun babban birnin tarayya Abuja ya ki amincewa da bukatar 'yan tsagin Ganduje kan batun soke zaben da su Malam Shekarau suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel