Oshiomhole: An tuge allon hoton Shugaban APC daga Sakariyar Jam’iyya
Allolin da ke dauke da hotunan Adams Oshiomhole sun fara yin kusufi a Sakatariyar jam’iyyar APC mai mulki kamar yadda rahotanni daga Daily Trust su ka bayyana.
Jaridar ta bayyana cewa an dauke katafaren allon da ke dauke da hoton Kwamred Adams Oshiomhole da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Hedikwatar APC.
Labarin da mu ka samu dazu shi ne a Ranar Laraba da dare, wasu su ka dauke allon shugaban jam’iyyar da aka dakatar, inda su ka maye gurbinsa da wani allon na dabam.
Kwanakin baya ne kotu ta bada umarnin dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa. Hakan ya nuna cewa akwai baraka a cikin jam’iyyar.
An maye gurbin wannan allo ne da wani mai dauke da hoton shugaban kasa Muhammadu Buhari. Haka zalika an tuge wasu allolin Oshiomhole da ke bakin titin ofishin.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya na halartar bikin da ake yi a Arugungu
Akwai wasu manyan alloli na Adams Oshiomhole da tambarin jam’iyyar APC a layin Blantyre. A wannan layi ne babban ofishin jam’iyyar APC na kasa ya ke a birnin tarayya.
A daidai lokacin da aka cire hotunan tsohon gwamnan na Edo, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada amincewarsa na cewa a kira taron majalisar NEC na jam’iyyar APC.
Ana tunanin cewa a taron majalisar zartarwar da za ayi, za a nada sabon mukaddashin shugaban jam’iyya wanda zai jagoranci ragamar APC kafin a gama shari’a a gaban kotu.
Masu hasashe su na ganin cewa idan har aka yi wannan taro, an kama hanyar yin waje da Oshiomhole daga kujerar jam’iyya, wanda hakan ya na da tasiri da siyasar 2023.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng