Yanzu-yanzu: Kotu ta jaddada dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban APC

Yanzu-yanzu: Kotu ta jaddada dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban APC

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A ranar 4 ga watan Maris ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar wasu mambobin APC shida na jihar Edo wajen dakatar da Oshiomhole.

Alkalan kotun da suka samu jagorancin shugaban alkalan kotun daukaka kara, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta yanke hukuncin cewa daukaka karar dakatar da Oshiomhole bata da tushe.

Wannan hukuncin na zuwa ne a ranar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fita daga jam'iyyar APC bayan ganawarsa da Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Obaseki ya gana da Gambari a kan hana shi takara da jam'iyyar APC tayi a ranar Juma'a. Jam'iyyar ta hana shi takara ne saboda banbance-banbance a takardun shaidar karatunsa.

KU KARANTA: Harin 'yan bindiga: Jama'a ta za su kare kansu idan FG ba za ta iya ba - Sanata

Bayan hana Obaseki takara, ya yi martani a kan sanarwar da kwamitin tantance yan takarar gwamnan na jamiyyar APC ta yi inda ta ce bai cika kaidojin shiga takarar ba.

Obaseki ya ce bai zai daukaka kara ba ko kai maganan gaba bisa korarsa daga cikin yan takarar da aka yi a zaben fidda gwani na jamiyyar da ake sa ran yi a watan Satumban wannan shekarar.

A sakon da ya fitar ta bakin kakakinsa, Crusoe Osagie, gwamnan ya ce tabbas ya ce yadda ake cin zarafin demokradiyya karkashin jagorancin kwamared Adams Oshiomhole a jami'yyarsa ta APC.

Gwamnan ya ce wannan lamarin abin takaici ne da bacin rai. Obaseki ya ce tun da farko ya san ba za ayi masa adalci ba duba da yadda mutum daya ke karya dokoki yana juya jami'yyar yadda ya ke so gabanin tantance 'yan takarar gwamnan na zaben Edo.

Obaseki ya cigaba da cewa abin kunya ne yadda "a fili ake cin zarafin demokradiyya, saba dokoki da rashin adalci" da Kwamared Adams Oshiomhole ya jawo a jami'yyar.

"Abin bakin ciki ne hakan ya rika faruwa a jamiyyar da ke ikirarin kawo canji da adalci," in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel