Bidiyo: Yadda Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Abokin Karatunsa a Amurka Ya Kayatar da Jama'a

Bidiyo: Yadda Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Abokin Karatunsa a Amurka Ya Kayatar da Jama'a

  • Mutane sun ɓarke da shewa da tafi a lokacin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da abokin karatunsa a Jami'ar Chikago
  • Tinubu ya bayyana wani ɗan kasuwa daga ƙasar Belarus, Alex a matsayin abokin karatunsa a wurin wani taro a birnin Abuja
  • Shugaban ƙasar ya ce a yanzu jami'arsu za ta yi alfahari da matakin da suka taka a rayuwa, duba da gudummuwar da suke bayarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da ɗaya daga cikim abokan karataunsa a Jami'ar Chicago da ke ƙasar Amurka.

Shugaba Tinubu ya gabatar da mutumin mai suna Alex a taƙaice, wani ɗan kasuwa a Belarus, yana mai cewa sun yi maƙwaftana a lokacin da suka yi karatu a Jami'ar jihar Chicago.

Kara karanta wannan

ADA: Atiku ya gana da 'yan Kanyywood, 'yan siyasar Arewa kan sabuwar tafiya

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Yadda Tinubu Ya gabatar da abokin karatunsa ya kayatar da jama'a Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa bidiyon lokacin da Tinubu ya gabatar da Alex cikin farin ciki da walwala a taron kaddamar shirin inganta noma a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya nuna abokin karatunsa

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa da sake haduwa da tsohon abokinsa kuma makwabcin shi a Jami’ar Chicago da ke jihar Illinois, Amurka, Alex.

A wajen taron, an ƙaddamar da manyan injinan noma guda 2,000 da sauran kayan aikin gona, a wani bangare na yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da ƙasar Belarus.

Wannna shiri dai an ɓullo da shi ne da nufin inganta aikin noma, yaki da talauci, da kuma tabbatar da samar da isasshen abinci a Najeriya.

Yadda Tinubu ya gabatar da ɗan makarantarsu

Taron ya samu halartar Mataimakin Firaministan Belarus, Viktor Karankevich, da kuma Alex Sigman, wanda yanzu ya zama babban dan kasuwa daga Belarus.

A cikin jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce:

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya tayar da kura bayan zargin Tinubu da mahaifiyarsa da rusa zaben Abiola

“Abokina na gaskiya kuma tsohon makwabci na, Alex Sigman, dole ne mu fayyace labarin nan. Mun yi karatu tare a Jami’ar Jihar Chicago.
“Ga dukkan ku, Alex aboki na ne sosai kuma mun zauna makwabta a Chicago. Mun je makaranta tare.
"A wancan lokacin, ba wanda daga cikinmu ya taɓa mafarkin cewa wata rana zan zama Shugaban Najeriya, shi kuma Alex ya zama sanannen ɗan kasuwa a Belarus.”
Shugaba Tinubu, Alex tare da abokan hulɗar Najeriya daga Belarus.
Shugaba Tinubu ya kaddamar da shirin inganta noma na Renewed Hope a Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

'Jami'ar Chicago za ta yi alfahari da mu'

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa lokacin da suke tare a Amurka, ba su taɓa tsammani za su taka matsayin da suke ba a yanzu, rahoton Channels tv.

"Yau ga shi abokina ya kawo haɗin gwiwa mai tasiri da za ta inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin ƙasashenmu biyu."
"Na yi imani jami’ar mu za ta yi alfahari da irin wannan ci gaba da muke samu a yau. Muna alfahari da abin da kake yi. Ina da tabbacin cewa kai ma kana farin ciki da abin da ke faruwa a yau. Allah ya ƙara maka kuzari," in ji Tinubu.

Kara karanta wannan

Kisan 'yan daurin aure a Plateau ya je kunnen Tinubu, ya ba da umarni

Tinubu yana ɗaukar daraussa daga ƴan adawa

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yana ɗaukar darussa na shugabanci daga masu fitowa fii suna sukarsa tare da gwamnatinsa.

Tinubu ya ce yana ɗaukar korafe-korafe da ra’ayoyin jama’a da matuƙar muhimmanci, yana kuma koyon abubuwan da suke daidai daga cikin sukar da ake yi masa.

A cewar mai girma shugaban ƙasar, ƴan adawar da suke yawan sukarsu ba su ganin ayyukan alherin da yake zuba wa ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262