Bayan Ganawarsa da Tinubu, Tsohon Gwamna Ya Yi Maganar Yiwuwar Barin PDP

Bayan Ganawarsa da Tinubu, Tsohon Gwamna Ya Yi Maganar Yiwuwar Barin PDP

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya kai ziyarar ban-girma ga Shugaba Bola Tinubu a gidansa dake Ikoyi yayin bikin Sallah
  • Fayose ya yaba wa Tinubu kan kokarinsa na ceto tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce ya ziyarci shugaban kasar domin karfafa gwiwarsa
  • Yayin da jiga-jigan PDP ke ci gaba da komawa APC, Fayose ya nanata cewa ba zai taba barin jam'iyyar ba duk da rikicin da take ciki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya kai ziyarar ban-girma ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Ikoyi, yayin bikin babbar Sallah.

A yayin ziyarar, jigo na jam'iyyar PDP, Ayodele Fayose, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan ƙoƙarinsa na ceto Najeriya daga rugujewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya fadi fannin da Tinubu ya yi wa abokan hamayyarsa zarra

Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya yabawa gwamnatin Tinubu kan tattalin arziki
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a Legas. Hoto: @OlayinkaLere
Source: Twitter

Fayose ya magantu bayan ganawa da Tinubu

A cewar Fayose, wannan ziyarar kashin kai ce kuma ya kawo ta ne don ƙarfafa gwiwar shugaban ƙasar kan ci gaba da inganta rayuwar ƴan Najeriya, inji rahoton TVC News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar, wanda ta ja hankalin 'yan siyasa, ta zo ne a yayin da ake fama da rikice-rikice a cikin jam'iyyar adawa ta PDP da kuma yawaitar sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

Fayose ya bayyana ziyarar a matsayin alamar haɗin kai da sada zumunci a cikin hutun babbar Sallah, yayin da ya sake tabbatar da imaninsa ga shugabancin Bola Tinubu.

Ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai amfani da gogewa wajen mulki da kuma amfani da zurfin tunani wajen magance matsalolin Najeriya.

Tattalin arziki: Ayo Fayose ya yaba wa Tinubu

Duk da cewa sauye-sauyen Tinubu ba su kawo sakamako nan take ba, amma Fayose ya ce manufofin shugaban kasar na kan hanya, kuma za su haifar da abin da ake nema a nan gaba.

Kara karanta wannan

'Hanya 1 da 'yan adawa za su bi domin kayar da Tinubu a 2027,' inji Dele Momodu

Fayose ya yaba wa shugaban ƙasar kan matakan da ya ɗauka na ƙarfafa tattalin arziki, yana mai cewa waɗannan manufofi sun ba 'yan Najeriya yakinin samun sabuwar rayuwa.

Yayin da mutane da yawa suka yi hasashen cewa ziyarar tasa na iya nuna shirin sauya sheƙarsa zuwa APC, Fayose ya yi hanzarin musanta irin waɗannan zato.

Fayose ya ce ba zai taɓa barin PDP ba

Channels TV ta rahoto tsohon gwamnan ya nanata matsayarsa ta baya, cewa ba zai taba ficewa daga PDP ba duk da cewa matsalolin jam'iyyar sun yi kamari, har kowa ma ya sansu.

Ya ce waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC sun yi hakan ne saboda dalilai daban-daban, ciki har da gamsuwa da aikin Tinubu da kuma rikicin da ke cikin PDP.

Ɗan siyasar mai faɗa a ji ya yarda cewa PDP "jam'iyyar na gargarar mutuwa," inda ya ce tana fama da rikicin cikin gida da aka gaza warwarewa da kuma rashin jagoranci.

"Na faɗa a baya kuma zan sake faɗa: 'Ranar da na yanke shawarar barin PDP ita ce ranar da zan bar siyasa gaba ɗaya'."

Kara karanta wannan

Bayan jita jita na yawo, Wike ya magantu kan masu juya akalar gwamnatin Tinubu

- Inji Fayose.

Kalli bidiyon Fayose a nan kasa:

'Dalilin marawa Tinubu baya a 2023' - Fayose

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya goyi bayan Shugaba Bola Tinubu ba wai don kwadayin muƙami ba.

Ya kuma shawarci duk masu burin ganin sun kawo karshen mulkin Tinubu da su haƙura kawai su rungumi ƙaddara.

Fayose ya ƙaryata zargin da ake yi na cewa gwamnonin G5 na jam'iyyar PDP sun kulla jarjejeniya da Tinubu don mara masa baya a zaɓen da ya gabata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com