"Ba Domin a Bani Mukami Na Marawa Tinubu Baya Ba", Ayo Fayose

"Ba Domin a Bani Mukami Na Marawa Tinubu Baya Ba", Ayo Fayose

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose yace ba ƙwadayin muƙami ya sanya shi marawa Bola Tinubu baya ba
  • Tsohon gwamnan ya kuma shawarci waɗanda ke son ganin sun raba Tinubu da kujerar sa kan su haƙura su rungumi ƙaddara
  • Fayose ya kuma ce baya da masaniya kan yarjejeniyar da gwamnonin G5 na jam'iyyar PDP suka ƙulla da Tinubu domin Mara masa baya a zaɓen shugaban ƙasa

Jihar Ekiti- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa goyon bayan sa ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ba domin kwadayin muƙami bane ba.

Fayose yayi gargaɗin cewa masu shirin raba tsohon gwamnan na jihar Legas da muƙamin sa, mafarki kawai suke yi inda yace zaɓe ya zo kuma har ya wuce. Rahoton Vanguard

Kara karanta wannan

Batun Hango Ranar Mutuwar Sa, Shahararren Fasto Ya Fito Ya Bayyana Gaskiyar Zance

Fayose
"Ba Domin a Bani Mukami Na Marawa Tinubu Baya Ba", Ayo Fayose Hoto: Punch
Asali: UGC

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa a wani shirin gidan talabijin na Channels Tv, mai suna Siyasa a Yau a ranar Talata. Rahoton Within Nigeria

Da yake amsa tambaya kan wace irin yarjejeniya ce aka ƙulla tsakanin gwamnonin G5 waɗanda suka marawa Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa, da ko akwai alƙawarin raba muƙamai, sai ya kada baki yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ni tsohon gwamna ne, a bayan gwamnoni masu ci nake tsayawa, sannan idan suka je taro bana kasancewa a wajen, amma matsaya ta itace idan ina goyon bayan ka, to da gaske nake yi ba wasa."
"Umurnin shine mu goyawa ɗan takarar da ya fito daga Kudancin Najeriya baya, saboda hakan shine matsayar gwamnonin da shugabannin da suka san abinda ya dace."
Ɗan takarar Kudancin Najeriya shine zaɓaɓɓen shugaban ƙasa kuma nayi adalci. Bana neman ko wane irin muƙami ido rufe, na yi gwamna har sau biyu, hakan ma ya ishe ni."

Kara karanta wannan

Sun Ki Allah Ya Nufa: Yadda Na Kusa Da Ni Suka Ci Amanata a Lokacin Zabe, Gwamnan APC Yayi Bayani Mai Sosa Rai

"Duk wanda yake tunanin zai iya raba Bola Tinubu da kujerar sa, to ya farka daga barcin da yake yi. Zaɓe ya zo kuma har ya wuce."

Amurka ta Jero Inda aka yi Aika-Aika a Zaben 2023, Ta Fadi Matakin da Za a Dauka

A wani labarin na daban kuma, ƙasar Amurka ta lissafo inda aka samu tarnaƙi a zaɓen 2023 da aka gudanar a ƙasar nan.

Ta kuma sanar da matakan da za ta ɗauka kan waɗanda ke da hannu a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel