ADC: Maganar Hadakar Adawa Ta Yi Nisa, Ana dab da Cimma Matsaya kan Zaben Jam'iyya

ADC: Maganar Hadakar Adawa Ta Yi Nisa, Ana dab da Cimma Matsaya kan Zaben Jam'iyya

  • Shugaban jam’iyyar ADC na kasa, Ralphs Okey Nwosu ya ce ana samun hadin kai a kan batun hadakar yan adawa gabanin 2027
  • Dr. Nwosu ya bayyana zuwa yanzu, kwamitocin da suka shiga tattaunawa da manyan ’yan siyasa da ƙungiyoyi sun kusa cimma matsaya
  • Ya ce jam'iyyar ADC ce hanyar da za a bi wajen ceto yan Najeriya, kuma nan da wasu kwanaki za a sanar da matsaya ta karshe

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa, Dr. Ralphs Okey Nwosu, ya bayyana cewa za a kammala tattaunawar kafa hadakar jam’iyyu cikin makonni biyu masu zuwa.

Hadakar ta bayyana cewa za ta iya amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin da za ta tsaya takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 don yakar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

LP: Ana maganar hadaka, Peter Obi ya fadi jam'iyyar da zai yi takarar 2027

Adawa
ADC ta ce ana duba batun hadakar yan adawa a Najeriya Hoto: @Omoluabi_sq
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Nwosu ya bayyana cewa kwamitocin da jam’iyyar ta kafa sun riga sun gana da waɗanda ke da ruwa da tsaki a kan maganar hadakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC: Ana tattaunawa hadakar adawa

The Cable ta ruwaito cewa Dr. Nwosu ya bayyana cewa akwai wata ganawa ta ƙarshe da za ta gudana tsakanin ƙungiyoyin al’umma, ƙungiyoyin fararen hula da sauran manyan masu ruwa da tsaki kan hadakar.

Ya ƙara da cewa kwamitin da jam’iyyar ta kafa ya riga ya gana da jiga-jigan 'yan siyasa da ke cikin shirin hadakar kamar Atiku Abubakar, Peter Obi da sauransu.

A cewarsa:

“Jam’iyyar ADC ta fara wannan tsari tun watanni 16 da suka wuce, kuma abin da muke yi shi ne, bayan tattaunawar siyasa da shugabanni, mun ga ya zama dole mu tabo tushe, domin halin da ƙasar nan ke ciki."

Nwosu: "ADC za ta kai Najeriya ga ci"

Kara karanta wannan

2027: An samu wanda zai buga da Tinubu, jigo zai fito takarar shugaban ƙasa a APC

Ya ce a halin yanzu, ’yan Najeriya masu kishin ƙasa na kallon ADC a matsayin dandalin hadakar da za ta kawo sauyin da ake bukata a ajeriya.

Amma ya jaddada cewa:

“Ba za ka iya tattauna batun shugabanci ko na siyasa a Najeriya cikin su kadai ba, don haka sai da aka kafa kwamitoci domin tattauna wa da jama’a."

Nwosu ya bayyana cewa siyasar ADC ta danganci sauyi da haɗin kai, yana mai cewa za a yi tattaunawar ne a kan matakai guda uku.

Atiku
Ana sa ran gama magana kan hadakar adawa da ADC a makonni biyu Hoto: AbdulRasheed Shehu
Source: UGC

Ya ƙara da cewa:

“Ni ne Shugaban jam'iyya na ƙasa kuma shugaban hukumar tuntuba da ke hulɗa da ’yan ƙasa da wasu masu kishin ƙasa. Aiki na ya bambanta da na sauran kwamitocin.”
“Dr. Bamidele Jamilu Jade, shi ne ke da alhakin ganawa da wasu ɓangarorin jam’iyyun siyasa. Dr. Mani Ibrahim Ahmad, shi ma na hulɗa da masu ruwa da tsaki daga cikin jam’iyyun siyasa.

An musanta zaben ADC a hadakar adawa

A baya, kun ji cewa hadakar siyasa ta nesanta kanta daga rahotannin da ke cewa ta zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin dandalin da za ta yi amfani da shi domin fafatawa a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Ana tunanin haɗaka a ADC, Atiku Abubakar ya jefa magoya bayan PDP a duhu

Salihu Moh. Lukman, wani jigo a cikin hadakar shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga Mayu, a birnin Abuja, kuma ya ce har yanzu ana tattauna batun.

A cewar Lukman, rahoton da ke cewa hadakar ta zaɓi ADC ko an naɗa shi a matsayin shugaban ofishin hadakar, “karya ce tsagwaronta” da ake yadawa don kawo masu rikici.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng