'Allah Ya Isa,' Shugaban PDP Ya Kausasa Harshe kan Zargin Yiwa APC Aiki
- Shugaban PDP na riko, Ambasada Umar Iliya Damagum ya ce bai da hannu a wani yunkuri na taimaka wa APC domin rage karfin jam’iyyarsa
- Ambasada Damagum ya fusata sosai, inda ya ce dukkanin masu zarginsa da yiwa APC aiki na son bata masa suna da rage tasirinsa a PDP ne kawai
- Shugaban, ya kara da cewa ba shi kadai ke da alaka da Nyesom Wike ba, wanda ake da yakinin yana yiwa jam'iyyar APC da Bola Tinubu aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya ta PDP, Ambasada Umar Iliya Damagun, ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewa yana da hannu a rikicin jam’iyyar.
Haka kuma, ya mayar da martani kan zargin da ake yi masa na yi wa jam’iyyar mai mulki, APC, aiki a boye domin kassara PDP da rage tasirinta.

Source: Twitter
Ambasada Damagun ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce game da zargin cewa shi dan-amshin-shata ne na jam'iyyar APC, "Allah ya isa."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban PDP ya musanta yi wa APC aiki
Damagun ya kara da cewa tuni aka dade ana yi masa sharri, inda ake zargin cewa yana taimaka wa APC domin rage karfin jam’iyyar hamayya ta PDP.
Ya ce:
"Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan kazafi, kuma Allah zai yi mana shari’a. In da zan shiga jam’iyyar APC, da tun zamanin Buhari na shiga.
"Kuma ina da tarihi tun daga lokacin da na shiga jam’iyyar PDP a 1999, ban taba sauya sheka ba. Dole wanda ba ya sona zai nemi hanyar da zai zarge ni don ya biya bukatarsa. An ce wai na je na yi taro da Tinubu a Ingila, duk masu irin wannan zargi, na bar su da Allah."
Damagum ya magantu kan alaƙarsa da Wike
Ambasada Damagun ya bayyana cewa ba shi kadai ba ne ke da alaka da Ministan Abuja, Nyesom Wike, a cikin jam’iyyar PDP ba.
Ya ce ana sukar sa ne saboda bai bayar da dama a juya Wike yadda wasu ke so ba. Sai dai ya tabbatar da cewa ba ya yi wa APC aiki kamar yadda ake zargi.

Source: Twitter
Game da yadda wasu manyan ‘yan PDP suka sauya sheka a baya-bayan nan, Damagun ya bayyana takaicinsa, tare da cewa za su yi kokarin dinke barakar da ta kunno kai.
Ya kara da cewa, daga cikin dukkanin wadanda suka sauya sheka, babu wanda ya bayar da hujja cewa an yi masa laifi a jam’iyyar.
Atiku Abubakar ya karyata shirin barin PDP
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP saboda hadakar adawa.
Wannan karin haske ya fito daga bakin hadiminsa na yada labarai, Paul Ibe, wanda ya bayyana cewa Atiku na ci gaba da tattaunawa da wasu fitattun 'yan adawa domin karfafa hadakar.
A cewar Atiku, ya riga ya bayyana matsayinsa na cewa zai ci gaba da kasancewa a cikin PDP, kuma wannan ba zai shafi shirin hadakar adawa da ake yi don korar Bola Tinubu daga ofis ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


