Ana tsaka da Rikicin Naɗin Galadiman Kano, Gwamna Abba Ya Fara Jin Ƙanshin Nasara a 2027
- Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano karƙashin kungiyar NLC sun goyi bayan tazarcen Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaben 2027
- Shugaban NLC na Kano, Kwamared Kabiru Inuwa ne ya bayyana hakan a bikin murnar zagayowar ranar ma'aikata ta duniya jiya Alhamis
- Ya ce Gwamna Abba ya cancanci a ba shi dama karo na biyu duba da dumbin nasarorin da ya samu tun da ya kafa gwamnati a Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), reshen jihar Kano, ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya zarce wa'adi na biyu a 2027.
Kungiyar Kwadagon ta yabawa mai girma gwamnan bisa irin kulawa da yake nuna wa wajen inganta walwala da jin daɗin ma'aikata da ƴan fansho a Kano.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya tabbatar da matakin da NLC ta ɗauka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar APC ta ƙara nakasa El Rufai da Kwankwaso, jiga jigai sun bar PDP da NNPP
2027: Gwamna Abba ya fara samun goyon baya
Sanarwar ta ce shugaban NLC na jihar, Kwamared Kabiru Inuwa, ne ya bayyana goyon bayan ma'aikata ga Gwamna Abba a bikin ranar ma'aikata ta duniya.
An dai gudanar da bikin ranar ma’aikata ta Duniya ne a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano, a ranar Alhamis, 1 ga Mayu, 2025.
A cewar Kwamared Kabiru Inuwa, Abba ya kafa tarihi a matsayin gwamna na farko a Najeriya da ya aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ₦71,000.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin jarumta kuma abin a yaba, wanda ya rage wa ma’aikata radadin halin ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arzikin da ake ciki.
Kungiyar NLC ta jero wasu nasarorin Abba
Ya kuma jinjinawa Abba Kabir bisa biyan albashi da fansho a kan lokaci ba tare da wata tangarda ba, gami da biyan bashin Naira biliyan 16 na hakkokin fansho da gwamnatin da ta gabata ta bari.

Kara karanta wannan
"Mutum mai gaskiya da rikon amana," Gwamna Radda ya sha ruwan yabo daga bakin Tinubu
Kwamared Kabiru ya kara da cewa ƙarin mafi ƙarancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000 wani babban mataki ne da ke nuna kulawar gwamna ga tsofaffin ma’aikata.
Baya ga gyaran al’amuran kudi, NLC ta kuma yaba wa mai girma gwamnan bisa daukar malaman makaranta, karin girma, da kuma zuba kuɗi a fannin fannin horar da ma’aikata.

Source: Facebook
'Gwamna Abba ya cancanci tazarce a 2027'
“Ina tabbatar da cewa wadannan nasarori ba alƙawurran da ya ɗauka kaɗai ba ne, illa dai shaidar yadda Gwamna Abba ke da gaske wajen kula da walwalar ma’aikata.
"Mai girma gwamna ya samu amincewa da goyon bayan ma’aikata a fadin jihar nan,” in ji Kwamared Kabiru Inuwa.
Wani ma'aikacin gwamnatun Kano, Isah Ahmad ya shaidawa Legit Hausa cewa za su sake marawa mai girma gwamna baya don ya shekara takwas a mulki.
Ya ce gwamnatin Abba ta yi abin azo a gani ta kowane fanni domin inganta walwalar jama'a.
Isah ya ce:
"Abba sai ya yi takwas da ikon Allah, mu ma'aikata muna daga cikin waɗanda suka amfana da tsare-tsaren gwamnatinsa.
"Idan ka duba kowane ɓangare kamar lafiya, ilimi, gina hanyoyi, tallafawa matasa da mata, Abba ya yi zarra, ina da yaƙinin zai sake samun nasara a 2027."
Gwamnatin Abba za ta kashe N51.5bn a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Abba Kabir ta amince da fitar da kudi Naira biliyam 51.5 domin gudanar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa.
Gwamnatin ta ware waɗannan kuɗaɗe ne a taron Majalisar Zartarwa ta jihar wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin Abba Gida Gida.
Ayyukan da za a yi da kuɗin sun kunshi gyaran tituna, faɗaɗa wasu gine-ginen gwamnati da inganta samar da wutar lantarki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
